Ambaliyar ruwa ta hallaka yara 4 a garin Abuja

Ambaliyar ruwa ta hallaka yara 4 a garin Abuja

Kananan yara hudu ne suka rasa rayukansu a wata mummunar ambaliyar ruwa da ta auku cikin al'ummar Dogon-Ruwa a yankin Abaji da ke babban birnin kasar nan na tarayya.

Manema labarai na jaridar Daily Trust sun ruwaito cewa, wata mata dauke da goyon jaririnta dan watanni shida da haihuwa, sun tsallake rijiya da baya yayin aukuwar ambaliyar ruwan a garin Abuja.

Wani mazaunin gari, Muhammadu Haruna, ya ce yaran da suka riga mu gidan gaskiya sun kasance a kan hanyar su ta komawa gida bayan dawowa daga cin kasuwar Lambatta inda motarsu ta dulmiye cikin ruwa.

Ya ce mummunan tsautsayin ya auku ne da misalin karfe 8.00 na dare a yayin da suke yunkurin tsallake wani rafi inda motar su ta mace, lamarin da ya ce "tsiyar karfen nasara sai za ka gida."

A cewarsa, kananan yaran hudu da suka riga mu gidan gaskiya sun kasance masu shekaru 7, 8, 9 da kuma 12. An gano gawawwakin su kwana guda bayan da ambaliyar ruwan tayi gaba da su.

KARANTA KUMA: An cafke wani mahaifi da laifin noma tabar wiwi a jihar Kebbi

A wani rahoto mai nasaba da wannan da jaridar Legit.ng ta ruwaito, jihohi 30 a Najeriya na fuskantar taraddadi na barazanar ambaliyar ruwa a sanadiyar yadda mafi akasarin su ke kusanci da kogin Neja da na Benuwe.

Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa na Najeriya, Injiniya Mustapha Maihaja, shi ne ya bayar da shaidar wannan lamari yayin zantawa da manema labarai tun a watan Agustan da ya gabata.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel