"Ina Roko": Jarumar Fim Ta ba Shugaba Tinubu Shawara kan Rashin Tsaro
- Shahararriyar jaruma a masana'antar Nollywood, Clarion Chukwurah, ta ba Shugaba Bola Tinubu shawara kan rashin tsaro
- Clarion Chukwurah ta yabawa shugaban kasar kan kokarin da ya yi wajen assasa kafa 'yan sandan jihohi a Najeriya
- Jarumar fim din ta bayyana cewa kafawa da tura 'yan sandan zai dauki lokaci, inda ta bukaci Shugaba Tinubu da ya bi wata hanyar ta daban don samar da tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shahararriyar 'yar wasan kwaikwayo ta Nollywood, Clarion Chukwurah, ta ba Shugaba Bola Tinubu shawara kan matsalar rashin tsaro.
Clarion Chukwurah ta yi kira ga Shugaba Tinubu da ya ɗauki matakan tsaro na ɗan lokaci cikin gaggawa domin magance karuwar rashin tsaro yayin da ake kan tsarin kafa 'yan sandan jihohi.

Source: Instagram
Jarumar fim din ta bayyana hakan ne cikin wata buɗaɗɗiyar wasiƙa da ta sanya a shafinta na Instagram ranar Laraba, 1 ga watan Yulin 2026.
Jarumar fim ta yabawa Tinubu
Chukwurah ta yabawa shugaban kasar bisa assasa kafa 'yan sandan jihohi, inda ta bayyana matakin a matsayin mataki na gari.
"Ina yaba wa gaskiyar cewa ka taɓa zama ɗan gudun hijira saboda dimokuraɗiyya a Najeriya da kuma matakin da ka ɗauka na kwanan nan don assasa kafa 'yan sandan jihohi domin yaƙi da rashin tsaro a ƙasarmu."
- Clarion Chukwurah
Ta bukaci a gaggauta daukar mataki
Sai dai jarumar ta bayyana cewa tsarin kafawa da kuma tura 'yan sandan jihohi gaba ɗaya a faɗin ƙasar, musamman a yankunan karkara, zai iya ɗaukar tsakanin shekara ɗaya zuwa biyu, yayin da matsalar rashin tsaro ke buƙatar daukar mataki cikin gaggawa.
"Yallaɓai, mun san tsarin da zai kai ga fara gudanar da ayyukanta na cikakken iko a kowace jiha zai ɗauki aƙalla shekaru ɗaya zuwa biyu, musamman wajen faɗaɗa ayyukanta zuwa ƙauyuka a yankunan karkara inda ayyukan masu garkuwa da mutane suka yi yawa kuma suke buƙatar mafita ta gaggawa."

Kara karanta wannan
Yadda shugaban ma'aikatar bogi ya rika tarurruka da manyan jami'an gwamnatin Tinubu
- Clarion Chukwurah

Source: Instagram
Wace shawara ta ba Tinubu kan rashin tsaro
Chukwurah ta buƙaci shugaban kasar da ya karkatar da wani ɓangare asusun tsaron kasa wajen ƙarfafa tsaron iyalai da al'umma ta hanyar ƙungiyoyin 'yan sa-kai masu ɗauke da makamai.
"Shugaban kasa, don Allah ka ba da umarnin yin amfani da wani ɓangare na biliyoyin kuɗaɗe na asusun tsaron kasa don tallafa wa tsaron al'umma ta hanyar 'yan sa-kai waɗanda aka ba su damar ɗaukar makamai don kare al'ummominsu."
- Clarion Chukwurah
Tinubu zai dauki matasa 5000
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana shirin gwamnatinsa na horar da matasa 5000.
Shugaba Tinubu ya ce za a horas da matasa 'yan Najeriya 5,000 a matsayin masu sanya mita da ƙwararrun masu aikin mita ƙarƙashin shirin PMI.
Tinubu ya ce an ƙirƙiri shirin ne domin samar da ayyukan yi, rage ƙarancin mita a faɗin ƙasar da kuma inganta samar da wutar lantarki.
Asali: Legit.ng
