Kotun Daukka Kara Ta Haramta wa Mata Musulmi Sanya Hijabi a Makarantar ISI Ta Najeriya
- Kotun daukaka kara ta soke hukuncin da ya ba dalibai mata Musulmai damar sanya hijabi a makarantar ISI da ke Ibadan
- Kotun ta ce makarantar ISI mai zaman kanta ce, don haka hukuncin Kotun Koli kan makarantun gwamnati bai shafe ta ba
- Daya daga cikin alkalan kotun ya saba wa wannan hukunci, inda ya nuna goyon bayan hukuncin halastawa dalibai sanya hijabi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Oyo, Nigeria - Kotun daukaka kara da ke zamanta a Ibadan ta haramtawa dalibai mata musulmi na Makarantar International School (ISI) da ke Jami'ar Ibadan sanya hijabi.
Kotun ta soke hukuncin Babbar Kotun Jihar Oyo, wacce ta amince dalibai mata su rika sanya hijabi a makarantar ISI tare da kayan makaranta.

Source: Getty Images
Leadership ta rahoto cewa kotun ta yanke wannan hukuncin ne ranar Juma'a a karar da mahukuntan makarantar suka daukaka domin kalubalantar hukuncin babbar kotun da aka yanke ranar 22 ga Mayu, 2024.

Kara karanta wannan
Babbar magana: Kotu ta ƙwace Naira miliyan 150 na wani 'dan Majalisar tarayya a Najeriya
Yadda aka fara takaddama kan hijabi
Shari'ar ta samo asali ne bayan dalibai mata Musulmai 11 sun shigar da kara suna zargin mahukuntan makarantar da tauye musu 'yancinsu na sanya hijabi a matsayin wani bangare na kayan makaranta.
Sai dai Kotun daukaka kara, da rinjayen alkalai biyu kan daya, ta amince da karar makarantar tare da soke hukuncin da babbar kotun Oyo ta yanke.
Hujjojin da kotu ta dogara da su
A cikin hukuncin da Mai Shari'a Biobele Georgewill ya karanta, wanda Mai Shari'a K.I. Amadi ya amince da shi, kotun ta ce Makarantar International School ta Jami'ar Ibadan makaranta ce mai zaman kanta.
Kotun ta bayyana cewa hakan ya bambanta ta da makarantun gwamnati da Kotun Koli ta taba yanke hukuncin amincewa mata su sanya hijabi.
Ya kara da cewa ba za a iya amfani da wannan hukunci kai tsaye ga makarantu masu zaman kansu ba, kamar yadda The Nation ta kawo.
Dalibai sun amince da dokokin makaranta
Kotun ta kuma bayyana cewa 'yancin gudanar da addini hakki ne na mutum wanda zai iya amincewa da wasu ka'idoji yayin shiga wata hukuma.
A cewar kotun, lokacin da daliban suka shiga makarantar sun amince da bin dokokinta, ciki har da tsarin kayan makaranta.
Mai shari'ar ya ce:
"A makarantun gwamnati ana iya sanya hijabi bisa hukuncin Kotun Koli, amma har yanzu Kotun Koli ba ta yanke hukunci kan sanya hijabi a makarantu masu zaman kansu ba."
Saboda haka, kotun ta soke hukuncin da ya bai wa dalibai mata Musulmai damar sanya hijabi a makarantar ISI.

Source: Getty Images
Alkali ya sabawa hukuncin
Sai dai Mai Shari'a Fadawu Umar ya saba wa wannan hukunci, yana mai bayyana cewa karar da aka shigar gaban kotun daukaka kara ba ta da inganci, don haka ya kamata a yi watsi da ita.
Ya kuma tabbatar da hukuncin Babbar Kotun Jihar Oyo da ya amince da hakkin daliban Musulmai na sanya hijabi a makarantar.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun nuna rashin imani, sun bude wa masu koyon karatun Alkur'ani wuta a Bauchi
An hana musulmi sanya hijabi a Austria
A wani labarin, kun ji cewa Majalisar dokoki a ƙasar Austria ta amince da sabuwar doka da ta haramta sanya hijabi ga yan mata Musulmi.
Sabuwar dokar ta samu amincewa ne da rinjayen ƙuri’u a zaman majalisar wacce ta haramta sanya hijabin ga yan mata a makarantu.
A karkashin sabuwar dokar, ’yan mata ƙasa da shekara 14 ba za su sake sanya gyale da ke rufe kai bisa al’adar Musulunci ba a dukkan makarantu.
Asali: Legit.ng
