'Yan kasuwar Kano sun nemi Buhari ya tsige shugaban hukumar Kwastam, Hameed Ali

'Yan kasuwar Kano sun nemi Buhari ya tsige shugaban hukumar Kwastam, Hameed Ali

Wasu 'yan kasuwar Singer da ke birnin Kanon Dabo, sun mika koko bara na neman shugaban kasa Muhammadu Buhari, da ya tsige shugaban hukumar hana fasa kwauri ta Najeriya, Kanal Hameed Ali mai ritaya.

Shugaban kungiyar matasan 'yan kasuwa ta Northern Young Marketers, Muhammad Bala Hotoro, shi ne ya yi wannan kira yayin hirarsa da manema labarai na jaridar Kano Today a ranar Alhamis ta makon da ya gabata.

Alhaji Hotoro wanda ya yi ikirarin cewa, wa'adin Kanal Ali a bisa kujerar jagorancin hukumar hana fasa kwauri ta kasar ya zo karshe tun a ranar 27 ga watan Agusta, bai yi wa 'yan kasuwar Arewa da kuma kasuwancin su adalci ba.

"Muna rokon shugaba Buhari ya nada matashi kuma wanda ya cancanta daga hukumar cikin jami'an hukumar kwastam, wanda ke da kyakkyawar masaniya ta al'amurran hukumar domin ci yar da kasar nan gaba da kuma bunkasar tattalin arziki." inji Alhaji Hotoro.

Alhaji Bala ya bayyana takaici gami da damuwa dangane da yadda da yawa daga cikin 'yan kasuwar Arewa suka fada kwatami da kuma samun karayar arziki a sanadiyar muzgunawa ta shugaban hukumar kwastam.

Ya yi babatun cewa, Kanal Ali na neman janyo durkushewar tattalin arzikin kasar nan a sanadiyar rashin yin gwanjon kayayyaki na fasakauri da hukumar kwastam ta cafke a tashohinta, lamarin da ya ce gwamnati za ta yi asarar miliyoyin dukiya mai tarin yawa.

KARANTA KUMA: Rashin Tsaro: Sufeto Janar na 'yan sanda ya koma Kudu maso Yammacin Najeriya

Haka zalika Mr Hotoro ya zargi Hameed Ali da rashin bayyana kadarori da dukiyar da ya mallaka a gaban kotun tabbatar da da'ar ma'aikata.

A sanadiyar hakan ne ya ke kira ga dukkanin masu yi wa Najeriya kyakkyawan fata, da su hada hannu-da-hannu wajen rokon shugaba Buhari a kan kada ya tsawaita wa'adin shugaban na hukumar Kwastam a bisa kujerar jagoranci.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel