'Yan daban daji sun sako mutane 30 da suka yi garkuwa da su a jihar Katsina

'Yan daban daji sun sako mutane 30 da suka yi garkuwa da su a jihar Katsina

A ranar Asabar da ta gabata ne gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya sake karbar wani kaso na mutum talatin da 'yan daban daji suka saki a yayin ci gaba tumke damarar yarjejeniyar sulhu da gwamnatin sa ta kulla da masu kai hare-hare a jihar.

A yayin da ba a bayyana kananan hukumomin mutane 4 da aka sako ba kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta bayar da shaida, 8 sun kasance 'yan karamar hukumar Kankara yayin da 18 suka fito daga yankin Shimfida na karamar hukumar Jibiya.

Daya daga cikin tubabbun 'yan daban daji da ya gabatar wa da gwamna Masari mutane talatin din a fadar gwamnatin Katsina, ya ce sun yi garkuwa da su ne a kauyen Dansadau na jihar Zamfara.

Ya ce wanda ya sace su ya kasance dan asalin karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara, inda ya ke cin karensa babu babbaka wajen tsintsintar mutane a jihar Katsina.

KARANTA KUMA: Karatun Al-Qur'ani yana kawar da damuwa da kuncin rayuwa - Ustaz Idris Ibrahim

Yayin da yake gabatar da jawabai ga wadanda suka kubuta, gwamna Masari ya ce zai ci gaba da jajirce wa wajen tabbatar da yarjejeniyar da gwamnatinsa ta kulla ta sulhu da masu kai hari domin sakin sauran mutanen jihar da aka yi garkuwa da su.

Gwamnan ya kuma bayar da umarnin duba lafiyar su a asibitoci da ke fadin jihar gabanin a sada su da 'yan uwansu.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel