Direbobi sun datse hanya a Kano kan cin zarafin 'yan KAROTA

Direbobi sun datse hanya a Kano kan cin zarafin 'yan KAROTA

Wasu direbobin motoci masu dakon kaya, sun datse babbar hanyar nan ta Bello Road dake cikin birnin Kanon Dabo, domin nuna adawa kan cin zarafin da jami'an hukumar KAROTA suka yi wa wani abokin aikin su.

Jaridar Kano Today ta ruwaito cewa, wannan hauragiya ta tsawon awanni uku ta auku ne a hanyar Ibrahim Taiwo da misalin karfe 2.00 na ranar Talatar da ta gabata, lamarin da ya sanya direbobi suka datse hanyar da ke kai wa zuwa kasuwar Singer da kuma ta Kantin Kwari.

Direban motar wanda hauragiyar ta auku a sanadiyarsa, Kabiru Muhammad, ya shaidawa manema labarai cewa, jami'an hukumar KAROTA sun kai mai cafka da laifin amfani da fitilun mota doriya a kan wadanda motarsa ta zo dasu.

Kamar yadda Kabiru ya bayar da shaida, jami'an KAROTA sun tursasa shi a kan cire wannan fitilu wanda a cewar su ya sabawa doka, inda ya zayyana masu cewa ba zai iya cire su ba nan take kasancewarsa bisa hanya a wannan lokaci.

Ya ke cewa, "ba tare na yi aune ba, na fara jin saukar duka inda suka yi min rubdugu da gorori kuma nan da nan na tsinci kaina tsamo-tsamo cikin jini."

Daya daga cikin direbobin da suka yi zanga-zanga, Auwal Yusuf, ya ce sun datse babbar hanyar ne domin nuna goyon baya da kuma bayyana rashin jin dadi a kan cin zarafin da aka yi wa abokin aikinsu.

KARANTA KUMA: An haramtawa ma'aikatan gwamnati buga waya a Senegal

Mr Yusuf ya ce ba za su lamunci wannan cin kashi da jami'an KAROTA ke yi ba na haramta masu walwala da kuma hakki na bil Adama.

Kakakin rundunar 'yan sandan Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, yayin bayar da tabbacin wannan lamari, ya ce ya umarci direbobin da su janye motocinsu daga hanya inda kuma ya ba da umarnin cafke dukkanin jami'an KAROTA da ke aiki a yankin domin bincikar lamarin.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel