'Shiru Ya Kare,' Ibrahim Dahiru Bauchi kan Kafa Masallatan Tijjaniyya a Jami'o'i
- Ana cigaba da ce-ce-ku-ce kan mallakawa 'yan Darikar Tijjaniyya masallatai da za su kebanta da su a jami'o'i domin yin amfani da su
- Daya daga cikin jagororin Darikar Tijjaniyya a Najeriya, Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi ya bayyana cewa ba su so a hada su da wasu a masallatai
- A wani kira da ya yi, ya bukaci a ba su fili su gina masallatai ko kuma jami'o'i su mallaka masu masallatan da za su rika ibada su-ya-su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Bauchi - Jagoran Ɗarikar Tijjaniyya a Najeriya, Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi, ya yi kira ga hukumomin jami'o'i da gwamnatin tarayya da su ware filaye ga mabiya Ɗarikar Tijjaniyya domin gina masallatansu.
Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi ya yi magan yana mai cewa hakan ne zai tabbatar da adalci da kuma ƙarfafa zaman lafiya a makarantun.

Source: Facebook
Albarka Radio ya wallafa bidoyon da ya ce Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi ya bayyana hakan ne yayin zikirin shekara-shekara da aka gudanar a birnin Lafiya na jihar Nasarawa a shafinsa na Facebook.
Maganar Ibrahim Dahiru Bauchi
Ibrahim Dahiru Bauchi ya ce mabiya ɗarikar sun daɗe suna haƙuri domin tabbatar da zaman lafiya, amma lokaci ya yi da za su nemi haƙƙinsu ta hanyar da ta dace.
A cewarsa:
"Mun ɗauka shirun da muke yi don a zauna lafiya ne, amma tunda abin ya kai haka, a ba mu haƙƙinmu. Kowace jami'a ta ba mu fili mu gina masallacinmu, ko kuma ta ware mana masallaci a cikin masallatan makaranta. Wannan shi ne zaman lafiya."
Shehin malamin ya ce a wasu lokuta ana korar mabiya Ɗarikar Tijjaniyya daga wuraren da suke gudanar da wazifa, ko kuma a dakatar da ayyukansu.
Yayin da ya ke magana kan bukatar ware masu masallaci, Ibrahim Dahiru Bauchi ya bayyana cewa ba su yarda wanda ya ya akidarsu su ya jagorance ba ko a hada su da wasu a masallaci, ya ce:
:Duk wanda ba akidarmu ɗaya ba, ba za mu yarda ya shugabance mu ba."
"Ba mu yarda ba... a ba mu namu kawai."

Source: Facebook
Maganar zaman lafiya a jami'o'i
Ibrahim Dahiru BAuchi ya yi magana game da cewa ba domin suna son zaman lafiya ba da yanzu wani labarin ake a jami'o'in kasar nan, ya ce:
"Don Allah idan 'yan Tijjaniyya muka ce ba za mu zauna lafiya ba, don Allah akwai wanda zai zauna lafiya a ƙasar nan? Amma kowa ya san mu mutane ne masu son zaman lafiya.
"Wallahi, da su ake hanawa abin da aka hana mu da yanzu duk makarantu ana yaƙi.
Ya yi barazanar cewa za su sigar da kara kotu a rusa kungiyar MSSN idan har lamarin ya cigaba ba tare da an dauki mataki ba.
ATBU ta dauki mataki kan masallatai
A wani labarin, mun kawo muku cewa hukumar jami'ar Abubakar Tafawa Balewa ta sanar da cewa ta dakatar da ibada a dukkan masallatai bayan sallolin farilla.
Kakakin jami'ar, Malam Zailani Bappah ya sanar da cewa sun dauki matakin ne domin ba kwamitin da aka kafa damar hada rahoto a mako biyu.
Matakin rufe jami'ar ya faro ne bayan Sheikh Mansur Isa Yelwa ya ajiye limanci kan ba 'yan Tijjaniyya fili su gina masallaci, inda ya za a raba kan jama'a.
Asali: Legit.ng


