'Yan daban daji sun sake kai hari jihar Neja

'Yan daban daji sun sake kai hari jihar Neja

Cikin tsawon lokacin da bai wuce sa'o'i 24 ba bayan kai hari kauyen Kukoki na karamar hukumar Shiroro a jihar Neja, 'yan daban daji sun sake kai wasu hare-hare kauyuka uku na karamar hukumar Rafi ta jihar da Yammacin ranar Talata.

Kauyukan da wannan sabon hari ya auku a cikin su kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito sun hadar da Rafin-wayam, Rafin-kwakwa da kuma Gidan Dogo-Gurgu.

Rahotanni sun bayyana cewa, maharan kimanin su 30 haye a kan babura 10 wanda kowanne ya dauko mutum uku-uku, sun watsa kauyukan uku inda mutanen gari suka arce unguwar Kagara domin neman mafaka a hedikwatar karamar hukumar Rafi.

Wani mashaidin wannan mugun lamari, Malam Dahiru, ya shaida wa manema labarai cewa, maharan bayan sun yi wa kauyen Rafin Wayam kawanya, sun kwashi burodi da kuma kayan shayi gabanin su danna kauyen Pangu Gari cikin takama.

KARANTA KUMA: 'Yan siyasa na gurgunta jami'o'in gwamnati a Najeriya - ASUU

Kwamishinan 'yan sandan jihar Neja, Adamu Usman, ya tabbatar da aukuwar wannan lamari yayin zantawa da manema labarai a ranar Laraba, lamarin da ya ce sun dukufa wajen gudanar da bincike domin damko masu hannun wajen aikata wannan ta'asa.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel