Babbar Magana: Kotu Ta Ƙwace Naira Miliyan 150 na Wani 'Dan Majalisar Tarayya a Najeriya

Babbar Magana: Kotu Ta Ƙwace Naira Miliyan 150 na Wani 'Dan Majalisar Tarayya a Najeriya

  • Babbar Kotun Tarayya ta ba da umarnin kwace Naira miliyan 150 da ake dangantawa da dan Majalisar wakilai, Hon. Nicholas Mutu
  • Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta ce kudin sun samo asali ne daga haramtattun ayyukan dan Majalisar
  • Bisa haka ne EFCC ta gabatar da bukatar kwace kudin gaba daya, kuma kotun ta amince da hakan bisa hujjojin da aka gabatar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ba da umarnin kwace Naira miliyan 150 da ake dangantawa da dan majalisar wakilai, Nicholas Mutu, tare da mika kudin ga Gwamnati Najeriya.

Hon. Mutu, wanda ke wakiltar mazabar Bomadi/Patani ta Jihar Delta a majalisar wakilai, ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC a tsakiyar shekarar 2025.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari ya rasa kadararsa bayan daurin shekaru 75 a gidan kaso

Nicholas Mutu.
Dan Majalisar wakilan tarayya daga jihar Delta, Nicholas Mutu Hoto: Hon. Nicholas Mutu
Source: Facebook

EFCC ta tabbatar da hukuncin kotu

Hukumar Yaki da Masu Yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta'annati (EFCC) ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X ranar Juma'a, 3 ga Yulin 2026.

A cewar hukumar, Mai Shari'a Joyce Abdulmalik ta yanke hukuncin ne bayan ta amince da bukatar EFCC na kwace kudin har abada.

Kotun ta ce bayan nazarin bukatun da aka gabatar da kuma bayanan rantsuwa daga lauyoyin ɗan majalisa da kamfaninsa, Airworld Technologies Ltd, ta gano cewa bukatar EFCC ta dace da doka.

Kotun ta yanke cewa kudin Naira miliyan 150 da Mutu ya mayar sun kasance kudaden da aka samu ta haramtacciyar hanya, saboda haka ta ba da umarnin mika su ga gwamnatin tarayya.

EFCC ta bayyana hujjojinta

EFCC ta ce ta gabatar da bukatar ne bisa tanadin Sashe na 44(2) na Kundin Tsarin Mulkin 1999 da kuma Sashe na 17 na Dokar Advance Fee Fraud and Other Related Offences ta shekarar 2006.

Kara karanta wannan

An mika wa Tinubu rahoto kan kara wa shugaban kasa da masu mukaman siyasa albashi

Hukumar ta kuma tuna cewa tun farko kotun ta bayar da umarnin kwace kudin na wucin gadi tare da umartar a wallafa sanarwar a wata jarida ta kasa.

Ta ce babu wanda ya gabatar da gamsasshiyar hujja da za ta hana a kwace kudin har abada.

Abin da binciken EFCC ya gano

A cewar EFCC, bincikenta ya nuna cewa Nicholas Mutu ya karbi cin hanci da ya kai Naira miliyan 400,159,689.63 daga kamfanin Starline Consultancy Services, wanda ke ba Hukumar Raya Yankin Neja Delta (NDDC) shawara.

Hukumar ta ce hakan ya faru ne lokacin da dan Majalisar ke shugaban kwamitin majalisar wakilai mai kula da NDDC.

EFCC najeriya.
Babbar hedkwatar hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC da ke Abuja Hoto: @OfficialEFCC
Source: Twitter

EFCC ta ce kudaden sun rika shiga asusun kamfanonin Airworld Technologies Ltd da Oyien Homes Ltd a Heritage Bank, inda aka yi zargin an halasta su.

Ta ce ɗan majalisar wakilan shi ne babban mai hannun jari kuma darakta a kamfanonin, yayin da matarsa da sauran 'yan uwansa ke rike da sauran hannayen jari.

EFCC na bincike kan gyaran matatun fetur

A wani labarin, kun ji cewa EFCC ta gurfanar da tsofaffin shugabannin matatun man fetur na Fatakwal da Warri gaban kotu.

Kara karanta wannan

Iyayen daliban da aka sace sun rusa kuka bayan ziyarar tawagar Zulum

Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawar ta gurfabar da mutanen biyu ne kan zargin halasta kudaden haram da suka shafi kudaden gyaran matatun mai na Najeriya.

Wannan mataki na zuwa ne a cikin binciken da EFCC ke yi kan shirin gyaran manyan matatun man fetur na Najeriya da aka kashe makudan kudade a kai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262