INEC Ta Yi Shafin Rajistar Katin Zabe Ta Yanar Gizo, Ta Kara Wa'adin Mako 2

INEC Ta Yi Shafin Rajistar Katin Zabe Ta Yanar Gizo, Ta Kara Wa'adin Mako 2

  • Hukumar zabe ta kasa (INEC) ta tsawaita wa'adin rajistar masu kaɗa ƙuri'a domin mallakar PVC da mako biyu, daga 10 zuwa 24 ga Yulin 2026
  • INEC ta ƙaddamar da sabon tsarin rajista masu zabe ta intanet da zai ba sababbin son mallakar PVC tura bayanan su
  • Hukumar zabe ta ce matakin na da nufin bai wa dukkan 'yan Najeriya da suka cancanta damar mallakar katin zabe na PVC sauƙi kafin 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta tsawaita wa'adin rajistar masu kaɗa ƙuri'a na dindindin (CVR) da mako biyu, inda ta mayar da ranar ƙarshe daga 10 ga Yuli zuwa Juma'a, 24 ga Yuli, 2026.

Kwamishinan Hukumar kuma Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da Ilimantar da Masu Zaɓe, Mohammed Kudu Haruna, ne ya bayyana hakan a daren Juma'a a Abuja.

Kara karanta wannan

Zargin badakalar Gbajabiamila: Jam'iyyar NDC ta mika bukata ga Tinubu da EFCC

Joash Amupitan a wajen taro
Shugaban INEC, Joash Amupitan. Hoto: INEC Nigeria
Source: Twitter

Legit Hausa ta tabbatar da cewa hukumar zabe ta wallafa labarin kara wa'adin a wani sako da ta wallafa a shafinta na Facebook.

Dalilin INEC na kara wa'adi

Ya ce an ɗauki wannan mataki ne bayan hukumar ta yi nazarin yadda aikin rajistar ke gudana tare da la'akari da ra'ayoyin ofisoshinta na jihohi, jam'iyyun siyasa, ƙungiyoyin fararen hula da sauran masu ruwa da tsaki.

A cewarsa, an fara aikin rajistar ne tun daga 18 ga Agusta, 2025, kuma an ƙara wa'adin ne domin bai wa 'yan ƙasa da suka cancanta amma ba su yi rajista ba ƙarin dama kafin gudanar da zaɓe masu zuwa.

INEC ta ce tsawaita wa'adin ya nuna aniyarta na tabbatar da cewa duk wani ɗan Najeriya da ya cancanta ya samu isasshen lokaci da dama don shiga kundin rajistar masu kaɗa ƙuri'a.

Sabon tsarin rajistar PVC

Baya ga tsawaita wa'adin, hukumar ta sanar da ƙaddamar da sabon tsarin rajista ta intanet da mutum zai iya yi da kansa ga sababbin masu rajista.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun bindige yaro dan shekara 10, sun sace matan aure a Sokoto

Hukumar ta ce sabon tsarin zai fara aiki daga Laraba, 8 ga Yuli, 2026, ta hanyar shafin rajista na CVR mai adireshin cvr.inecnigeria.org, inda kuma za a samu cikakken bayani kan yadda ake yin rajistar mataki-mataki.

INEC ta bayyana cewa wannan tsarin zai ba wa waɗanda suka cancanta damar farawa da kuma kammala rajistarsu, har da ɗaukar bayanansu, ta amfani da wayoyi ko kwamfutocinsu ba tare da zuwa ofishin hukumar ba.

Jami'an hukumar zabe ta kasa
Yadda aka gudanar da zabe a Anambra a 2025. Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Ta ƙara da cewa tsarin ya ƙunshi tantance asali, tabbatar da sahihancin bayanan halitta da sauran matakan kariya domin tabbatar da inganci da amincin kundin rajistar masu kaɗa ƙuri'a.

INEC ta karbi sunan Atiku

A wani labarin, mun kawo muku cewa jam'iyyar ADC ta tabbatar da cewa ta daura sunan Atiku Abubakar a shafin hukumar zabe mai zaman kanta.

Kakakin jam'iyyar, Bolaji Abdullahi ne ya bayyana haka, inda ya sanar da manema labarai cewa sun daura sunan Rotimi Ameachi a shafin.

Hakan na zuwa ne yayin da jam'iyyun siyasa ke cigaba da shirye-shirye domin fuskantar juna a babban zaben shekarar 2027 da ke tafe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng