Tinubu Ya Fadi Wani Yanki a Arewacin Najeriya da Ke da Tasiri a Gwamnatinsa

Tinubu Ya Fadi Wani Yanki a Arewacin Najeriya da Ke da Tasiri a Gwamnatinsa

  • Shugaban kasa, Bola Tinubu ya bayyana wani yanki da yake da muhimmanci ga gwamnatinsa a Najeriya
  • Tinubu ya bayyana cewa ana gudanar da manyan ayyukan hanyoyi 61 a yankin wanda ya inganta rayuwar al'umma
  • Shugaban ya ce an kammala ayyuka biyar, yayin da ake ci gaba da manyan ayyuka 25 da kuma ayyukan gaggawa 31 a jihohin yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi magana kan wani muhimmin yanki a Arewacin Najeriya a gwamnatinsa.

Tinubu ya bayyana cewa yankin Arewa ta Tsakiya na da matukar muhimmanci ga gwamnatinsa, yana mai cewa ana gudanar da ayyukan hanyoyi 61 a jihohi shida na yankin.

Tinubu ya fadi abin alheri da ya yi a Arewa
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya yana jawabi a Abuja. Hoto: Asiwaji Bola Tinubu.
Source: Facebook

Tinubu ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da aikin gyaran hanyar Babban-Lamba zuwa Sharam kashi na biyu a karamar hukumar Kanke da ke Plateau, ta bakin shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Minista ya fadi abin da ke bata masa rai game da yan kasa kan gwamnatin Tinubu

Ayyukan da Tinubu a Arewa

Ya ce an riga an kammala ayyuka biyar, yayin da ake ci gaba da manyan ayyukan hanyoyi 25 da kuma ayyukan hanyoyin gaggawa 31 a fadin yankin Arewa ta Tsakiya.

A cewarsa, jihohin yankin ba su taba cin gajiyar irin wannan gagarumin shirin raya ababen more rayuwa daga gwamnatin tarayya kamar yadda ake yi yanzu ba.

Ya kara da cewa mafi yawan manyan hanyoyin da ake ginawa za su hada Arewa maso Yamma, Arewa maso Gabas, Arewa ta Tsakiya, Kudu maso Kudu, Kudu maso Gabas da Kudu maso Yamma.

Tinubu ya ce:

"Kowane yanki na Najeriya yana hade ta hanyar manyan ayyukan tarihi guda hudu na wannan gwamnati. Ba a taba yin irin haka ba."

Ya bayyana cewa wannan shi ne mafi girman shirin gina hanyoyi a tarihin Najeriya, yana mai cewa sauye-sauyen tattalin arziki sun fara inganta gudanar da mulki.

A cewarsa, alamomin tattalin arziki suna kara inganta, GDP na habaka, ajiyar kudaden ketare ta karu, yayin da yanayin zuba jari a Najeriya ya samu ci gaba sosai.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fara gina babbar hanya, za ta ratsa jihohin Arewa 5

Minista ya magantu kan hanyoyi a Najeriya
Ministan ayyuka a Najeriya, Dave Umarhi. Hoto: Federal Minstry of Works.
Source: Twitter

Umahi ya yabawa gwamnatin APC

A nasa jawabin, Ministan Ayyuka, Sanata David Umahi, ya ce APC na da dalilin farin ciki a Plateau da daukacin Arewa ta Tsakiya saboda yankin na da mafi girman shirin gina hanyoyi.

Umahi ya ce gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta mayar da hankali sosai wajen bunkasa hanyoyi a yankin, wanda zai taimaka wajen habaka tattalin arziki da saukaka zirga-zirga.

Ya kuma bukaci masu adawa, musamman dan takarar shugaban kasa na NDC, Peter Obi, da su rika yin suka masu amfani maimakon su yi suka marasa amfani, cewar Punch.

Yadda Tinubu ya amince a dauki ma'aikata

An ji cewa Fadar shugaban kasa ta fito ta bayyana cewa ba ta san da hukumar PFIPC ba wadda Adeniyi Adeyemi ke ikirarin jagoranta.

Ta bayyana shi a matsayin dan damfara, inda ta nuna cewa ya yaudari babban bankin Najeriya (CBN) wajen bude asusun banki.

Sai dai, wasika da aka gani, ta nuna cewa gwamnatin tarayya ta amince a dauki ma'aikata har guda 300 a hukumar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.