An yi mummunar arangama tsakanin 'yan sanda da mabiya akidar shi'a a jihar Katsina

An yi mummunar arangama tsakanin 'yan sanda da mabiya akidar shi'a a jihar Katsina

Mun samu cewa a yau Talata cikin binrin Katsinan Dikko, an yi mummunar arangama tsakanin jami'an hukumar 'yan sanda da kuma mambobin kungiyar IMN wadda aka fi sani da shi'a, inda da dama suka shiga hannu yayin da kuma wasu suka jikkata.

Kakakin kungiyar shi'a reshen jihar Katsina, Dr Abdulkarim Usman Abdulmumin, shi ne ya labartawa manema labarai na jaridar The Nation wannan rahoto a yayin zantawa ta hanyar wayar tarho.

Dr Usman ya zayyana cewa tattakin da suka fara gudanar wa da misalin karfe 7.30 na safiya, ya karke cikin gaggawa babu shiri a yayin da jami'an 'yan sanda suka tarwatsa su ta hanyar amfani da barkonon tsohuwa da kuma harbe-harben harsashin bindiga cikin iska

A yayin da babu ko rai daya na mabiya akidar shi'a da ya salwanta, sai dai kakin kungiyar ya ce jami'an tsaro sun yi wa mambobin su da damu jina-jina a yayin da kuma wasu suka shiga hannu.

Jagoran kungiyar shi'a reshen jihar Katsina, Malam Yakubu Yahaya, yayin zantawa da manema lababrai, ya kirayi al'ummar Najeriya da su fahimci akidun kungiyarsa da kuma manufofi, lamarin da ya ce sun kasance Almajirai ga jagoran su, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky.

Ya ke cewa, "kungiyar mu ba ta da wata manufa face tabbatar da ci gaban addini bisa fahimta ta irin ta akidar mu ko ina a fadin duniya, kuma wannan tattakin mun saba gudanar da shi a kowace shekara."

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, a yau 10 ga watan farko a shekarar Musulunci, aka sa ran mabiya kungiyar IMN wadda aka fi sani da shi'a a Najeriya, za su gudanar da tattaki na tunawa da kuma nuna juyayin mutuwar Imam Hussaini ibn Ali, wanda aka kashe a yayin yakin Karbala shekaru fiye da dubu daya da suka gabata.

Ilahirin mabiya akidar shi'a a fadin duniya na gudanar da wannan tattaki domin nuna bakin cikin su a wannan rana ta 10 ga watan Al-Muharram, domin nuna bakin cikin a kan mutuwar Imam Hussain wanda ya kasance jikan Manzn Tsira, Annabi Muhammad (Salallahu Alaihi Wasallam).

A wani rahoto da muka samu daga jaridar The Punch, rundanar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Kano, ta jibge fiye da jami'ai 200 a cikin birnin Kanon Dabo domin hana tattakin 'yan kungiyar shi'a, lamarin da ta ce ba za ta bari a gudanar da duk wani abu mai barazana ga zaman lafiya a kasar ba.

KARANTA KUMA: Manchester City ta fi kowace kungiya tara 'yan kwallo mafiya tsada a duniya

Cikin wata sanarwa da sa hannun kakakin rundunar 'yan sandan Kano, DSP Abdullahi Haruna, ya ce kwamishinan 'yan sandan Kano, Ahmed Iliyasu, ya yi gargadin cewa duk wanda aka kama ya sabawa dokar haramta duk wani tattaki zai fuskanci fushin hukuma.

A na iya tuna cewa, a baya-bayan nan sufeto janar na 'yan sanda Muhammad Adamu, ya bayar da umarnin haramta duk wasu al'amura na kungiyar shi'a a Najeriya, lamarin da ya ce kungiyar haramtacciya ce kuma ba za ta karbu ba a kasar.

Sai dai a na ta bangaren, kungiyar shi'a cikin wata sanarwa da ta fito daga bakin kakakin ta, Ibrahim Musa, ta ce babu gudu babu ja da baya akan gudanar da tattakin ta kamar yadda ta saba a kowace shekara, inda take cewa ba za a hana ta addini ba domin kuwa kundin tsarin mulkin kasa ya ba ta izini.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel