An cafke wani mahaifi da laifin noma tabar wiwi a jihar Kebbi

An cafke wani mahaifi da laifin noma tabar wiwi a jihar Kebbi

Hukumar yaki da ta'ammali da miyagun kwayoyi ta Najeriya NDLEA, ta cafke wani uban 'ya'ya shida mai shekaru 40, Abdullahi Sani, da laifin noma tabar wiwi a wata gonarsa da ke kauyen Shingi na karamar hukumar Danko/Wasagu a jihar Kebbi.

Shugaban hukumar NDLEA reshen jihar, Peter Odaudu, yayin zantawa da manema labarai a ranar Juma'a ya bayyana cewa, wannan katafariyar gona ta kasance ta biyu ta fuskar girma wadda a aka gano a tarihin jihar Kebbi.

Biyo bayan wani bincike da leken asiri, tawagar jami'an hukumar NDLEA sun gano wannan katafariyar gona a ranar 5 ga watan Satumba kuma suka halakar da ita nan take a kauyen na Shingi kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Babban jami'in hukumar ya bayyana damuwa dangane da yadda sannu a hankali jihar Kebbi ke neman sauya zani daga jiha mai ta'ammali da tabar wiwi zuwa jiha mai noma wannan hatsabibiyar ciyawa.

Hakazalika Mista Odaudu ya ce hukumar a ranar 24 ga watan Yulin 2018, ta cafke wani mai ba da magungunan gargajiya, Arage Rikici, da laifin noma tabar wiwi a wata gona da ke cikin kauyen Kukin a karamar hukumar Fakai ta jihar.

KARANTA KUMA: Mahara sun kashe mutane 2 a jihar Filato

A sanadiyar hakan ne babban jami'in hukumar ke gargadin manoman jihar da su kauracewa noma amfanin gona da suka sabawa doka, lamarin da ya ce noma tabar wiwi tana rage ingancin kasar noma.

A yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai a ofishin hukumar NDLEA da ke Birnin Kebbi, Abdullahi yayin tunatar da mahukunta cewa yana da mata da kuma 'ya'ya shida, ya nemi afuwa tare da rantsuwar cewa ba zai sake aikata wannan babban laifi ba.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel