Rashin Tsaro: Babu sauran aminci a Najeriya - Wamakko

Rashin Tsaro: Babu sauran aminci a Najeriya - Wamakko

Tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, ya yi Allah wadai dangane da yadda al'amura na rashin tsaro suka yi wa kasar nan dabaibayi, lamarin da ya ce 'yan Najeriya su dukufa wajen gudanar da addu'o'i na asamun aminci.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, Sanata Wamakko ya ce komawa ga Allah wajen ci gaba da kwarara addu'o'i ita kadai ce hanyar da Mai Duka zai jibinci yadda al'amura na tsaro suka tabarbare a kasar.

Da ya ke gabatar da jawabai ga magoya bayan jam'iyyarsa ta APC a harabar gidansa da ke Gawon Nama a birnin Shehu, Sanata Wamakko ya ce a halin yanzu babu sauran aminci da rage a kasar sanadiyar yadda 'yan Najeriya ba su da wadataccen tsaro a tafe bisa hanya ko kuma a cikin gidajensu.

A cewarsa, al'amura na rashin tsaro daban-daban da suka hana ruwa gudu a kasar nan sun hadar da kashe-kashe na babu gaira babu dalili, sace-sacen shanu, garkuwa da mutane tare da neman kudin fansa, fashi da makami da sauran miyagun ababe na ta'ada.

KARANTA KUMA: Boko Haram: Yi wa doka da'a ya sa Jonathan ya fasa tsige gwamnonin wasu jihohi 3 na Arewa

Ya kara da cewa, babu abinda sanya aminci a zukatan 'yan Najeriya face su tashi su nemi tsira a wurin Allah Madaukakin Sarki domin kuwa shi kadai ke da ikon jibintar lamarin su tare da magance kalubalai da kasar ke fuskanta.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel