Mutumin da Ya Sayar da Yaron Abokinsa a kan N1.3m Ya Tona Yadda Suke Cinikin Yara a Najeriya
- Rundunar yan sandan Najeriya ta bayyana cewa an kama wani da ake zargi da safarar yara, wanda ya amsa bayyana yadda suke cinikin bayin Allah
- Mutumin mai suna Sunday Onome ya ce suna sato yara daga sassa daban-daban na Najeriya sannan su sayar da su ga masu bukata
- Mutumin wanda ya bayyana yadda ya sace yaron abokinsa, sannan ya sayar da shi a kan Naira miliyan 1.3 ya fadi dalilin da ya sa shi danyen aiki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Anambra– Wani da ake zargi da safarar yara mai suna Sunday Onome ya bayyana wa jami'an tsaro cewa ya sayar da ɗan wani abokinsa kan kuɗi Naira miliyan 1.3.
Wannan na daga cikin ayyukan da wata ƙungiyar safarar yara da ake zargin tana aiki tsakanin jihohin Najeriya inda ake raba yara da iyayensu.

Kara karanta wannan
Allahu Akhbar: Babban likita ya rasu mintuna 15 bayan ya zo duba marasa lafiya a Kano

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa rahotanni sun nuna cewa jami'an IRU da VCRU na rundunar 'yan sandan Najeriya ne suka kama Onome a garin Onitsha na jihar Anambra.
Wani ya yi safarar dan abokinsa
The Sun Nigeria ta ruwaito cewa an kama wanda ake zargi tare da budurwarsa da kuma ɗansa yayin wani samame da jami'an suka kai, inda kuma suka ceto yara biyu da ake zargin an shirya safararsu.
A cewar wanda ake zargin, ya shiga ayyukan safarar yara fiye da sau ɗaya, kuma ya ce ya samu jimillar Naira miliyan 3.6 daga ayyuka biyu da ya gudanar.
Ya yi ikirarin cewa cinikin farko da ya shiga ya shafi ɗan wani amininsa, wanda ya ce ya miƙa wa wasu 'yan ƙungiyar safarar yara bayan ya karɓi Naira miliyan 1.3.
Onome ya ce bayan rasa aikinsa na direban haya ne matsin tattalin arziki ya sa ya haɗu da mutanen da ke gudanar da wannan haramtacciyar sana'a.
An gano kungiya mai safarar yara
Wanda ake zargin ya kuma bayyana cewa daga baya ya ƙara shiga harkar sosai bayan ya fara hulɗa da wata mata da ake zargin tana jagorantar wasu ayyukan ƙungiyar tare da shi.

Source: Original
A cewarsa, ayyukan da suka biyo baya sun haɗa da jigilar yara daga wata jiha zuwa wata, inda ake ba su umarni ta waya, sannan ana tura kuɗin aikinsu kai tsaye zuwa asusun bankinsa bayan sun kammala aikin.
Ya kuma yi zargin cewa budurwarsa tana taimakawa wajen tsara yadda ake gudanar da safarar, yayin da ɗansa ke taimakawa wajen kai yara wuraren da aka tanada kafin a miƙa su ga wasu mutane.
Yan sanda na bincikien safarar yara
Rundunar 'yan sanda ta bayyana cewa har yanzu bincike na ci gaba domin tantance ikirarin wanda ake zargin, gano sauran 'yan ƙungiyar da kuma fahimtar yadda take gudanar da ayyukanta.
Hukumar ta ce wannan na daga cikin matakan da take ɗauka na yaƙi da safarar yara, tana mai gargadin cewa masu aikata irin waɗannan laifuffukan na amfani da alaƙar aminci da kuma hanyoyin da ba na hukuma ba wajen yaudarar mutane.
Yan sanda sun jaddada cewa bincike bai kammala ba, kuma duk waɗanda aka kama ana ɗaukarsu marasa laifi ne har sai kotu ta tabbatar da akasin haka.
An kama jami'a kan zargin satar yara
A baya, mun samu labarin cewa an kama wata 'yar sanda mataimakiyar sufritanda, Kulu Dogo da makociyarta Elizabeth Oja bisa zargin satar yara domin safararsu zuwa sassa daban-daban a Najeriya.
Ana zargin sun hada baki wajen sace yara biyar daga jihar Sakkwato, bayan mutanen gari sun sanar da hukumomi alamun rashin gaskiya a tattare da su kuma suna bukatar a bincike su da kyau.
Gwamnatin jihar Sakkwato ta karbi yaran yayin da rundunar yan sandan jihar ta zurfafa bincike domin tabbatar da laifin da kuma gano girman mummunan aikin da suke aikata wa na sace yaran jama'a.
Asali: Legit.ng

