An cafke matashin da ya cilla jariri cikin ruwa a jihar Neja

An cafke matashin da ya cilla jariri cikin ruwa a jihar Neja

Hukumar jami'an tsaron cikin gida ta Najeriya NSCDC, a ranar Talata 10 ga watan Satumban 2019, ta cafke wani matashin dan acaba mai shekaru 20 kacal a duniya, Aliyu, da laifin cilla jaririnsa dan watanni hudu da haihuwa a cikin rafi.

Kwamadan hukumar NSCDC reshen jihar Neja, Mr George Edem, shi ne ya bayar da tabbacin wannan mummunan rahoto da cewar wanda ake zargi ya aikata laifin ne a kauyen Tamanine na karamar hukumar Borgu a jihar.

An tattaro cewa, ya zuwa yanzu ba a gano gawar jaririn ba duk da binciken da jami'ai suka dukufa wajen gudanarwa kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

Mr Edem ya ce za a mika Aliyu a hannun hukumar 'yan sanda domin ci gaba da binciken wannan lamari da rataya a wuyanta.

A nasa bangaren, Aliyu ya ce ya jefar da jaririn ne a bayan ya yi sukuwa a kan dokin zuciya sanadiyar yadda mahaifiyarsa da kuma mahaifiyar budurwarsa suka dora masa karan tsana tun bayan haihuwarsa watanni kadan da suka gabata.

KARANTA KUMA: Buhari ya kebance da shugaban Red Cross a fadar Villa

Ya ce bakin cikin yadda mahaifiyarsa a kullum take barazanar tsinewa jaririn da kuma buduwarsa wadda a kullum take cikin zubar hawaye a sanadiyar yadda mahaifiyarta ta kyamaci jaririn, ya sanya ya yanke wannan danyen hukunci.

A yayin da ya ke nadamar wannan mummunar ta'asa da ya aikata, Aliyu ya ce a shirye yake domin fuskantar duk wani hukunci da doka tayi tanadi.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel