Farfesa Ango Abdullahi ya nuna damuwarsa a kan matsalolin Fulani makiyaya

Farfesa Ango Abdullahi ya nuna damuwarsa a kan matsalolin Fulani makiyaya

- Farfesa Ango Abdullahi, tsohon shugaban jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, ya nuna damuwarsa a kan matsalolin Fulani makiyaya

- Dattijon arewan ya ce har amfani ake da rikicin Fulani makiyaya don cimma manufofin siyasa

- Ya yi kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya yi kokarin karfafa bangarorin da ba na gwamnati ba don rage rashin aikin yi da ya addabi kasar

Dattijon arewa, Farfesa Ango Abdullahi, ya jajanta kalubalen da Fulani makiyaya ke fuskanta a Najeriya. Ya shawarci Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya maida hankali akan matsalolin.

Ango, tsohon shugaban jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, ya shawarci gwamnatin tarayya data gyara wajajen kiwo 600 da aka banzatar dasu a arewacin kasar nan don rage matsalar.

Ya sanar da hakanne a ranar Laraba ga manema labarai a jihar Bauchi.

DUBA WANNAN: Gwamnatin Tarayya ta saba take umarnin kotu - Femi Falana

Ya ce: "Abinda ke faruwa ga Fulani makiyaya a fadin kasar nan ya ma koma siyasa. Duk wani abinda ya faru a kasar nan yanzu, Fulani makiyaya ne; sun manta da cewa Fulani makiyaya basu samun komai daga gwamnati."

"Fulani makiyaya sunfi morewa lokacin da turawa Duke. Turawa sunyi wa Fulani makiyaya hanyoyinsu, asibitin dabbobi, kasuwannin shanu da sauransu. Sun san cewa tattalin arzikin Najeriya ya dogara ne ga noma da kiwo."

"Ku duba irin tallafin da manoma ke samu; ku duba makiyaya, babu wani tallafi da yake zuwa musu,"

"Da yawa daga cikin dokokin noma da kiwo duk an barsu; Akwai wajen kiwo har 600 da aka banzatar dasu a arewa kawai. Akwai bukatar a gyarasu. Idan tunanin wannan ne karamin abu da za kayi ma Fulani."

Ango, daya daga cikin dattawan arewa, yayi kira ga gwamnatin tarayya da tayi wani abu don karfafa bangarori da ba na gwamnati ba. Hakan kuwa zai zama wata hanya ta samjn aiki don kawo karshen rashin aikinyi da ya addabi kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel