Osinbajo ya bude kasuwar shanu da katafariyar tashar mota a jihar Kebbi (Hotuna)
A ranar Alhamis, 12 ga watan Satumba, 2019, mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ziyarci jihar Kebbi domin kaddamar da wasu muhimman aiyuka.
A cikin sanarwar da fadar shugaban kasa ta fitar a shafinta na Tuwita, ta ce Osinbajo tare da gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu, sun kaddamar da bude katafariyar kasuwar zamani ta 'Ambursa, wata tashar motoci da kuma kasuwar shanu.
Kazalika, sanarwar ta bayyana cewa mataimakin shugaban kasar ya samu damar gana wa da wadanda suka ci moriyar tsarin bayar da tallafin N10,000 ga masu kananan sana'o'i tare da kaddamar da wata cibiyar kula da kananu da matsakaitun masana'antu (SMEs).
DUBA WANNAN: Gwamonin arewa sun fara gudanar da taro domin nema wa yankinsu mafita
A cikin hotunan da sanarwar ke dauke da su, an ga wasu daga cikin 'yan kasuwa a jihar Kebbi, sanye da rigar shirin bayar da tallafi ga masu kananan sana'o'i, na yin jinjina ga Farfesa Osinbajo.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng