Arewa
Wani hakimin gari ya hadu da fushin shugaban karamar hukuma bayan da ya lakadawa matarsa duka har ta mutu. An ruwaito cewa, yanzu haka yana hannun 'yan sanda.
Wasu 'yan bindiga sun hallaka mutane sama da 11 a wani yankin jihar Katsina. An ruwaito cewa, sun kuma jikkata mutane 3 a yayin harin da suka yi ta harbe-harbe.
Jihar Katsina ta tattara wasu mabarata da suka tare a filin wata makaranta a jihar. Sun ce suna neman abinci ne, don haka gwamnati ta basu tallafin buhun hatsi.
Kungiyar tuntuba ta arewa ta bayyana adawarta ga biyan kudin fansa ga 'yan bindiga. Kungiyar ta ce tana goyon bayan a tattauna amma ba ta goyon bayan fansa.
Rahoto ya bayyana yadda wasu matasa ke shan muggan kwayoyi da nufin rage radadin yunwa a watan Ramadana. Malamai sun yi Allah wadai da halayyarsu na shan kwaya.
Hatsarin jirgin ruwa ya yi sanadiyyar rasa rayukan wasu mutane 15 tare da samun wasu da suka jikkata sakamakon nutsewa a wani yankin jihar Neja a Najeriya.
An sako shugaban kungiyar Miyetti Allah da ake zargin an sace a ranar Talatan makon da ya gabata. Ya bayyana cewa, ba 'yan bindiga ne suka sace shi ba, wasu ne.
Darakta Janar na hukumar kula da sararin samaniya ya bayyana cewa, Najeriya na bukatar samun karin tauraron dan Adam wajen tabbatar da kame masu aikata laifuka.
Tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo ya shawarci gwamnatin Buhari kan hanyoyin da za a bi don tabbatar da an magance matsalar tsaro da kasar ke yi.
Arewa
Samu kari