'Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane 11, Sun Jikkata 3 a Kauyen Katsina

'Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane 11, Sun Jikkata 3 a Kauyen Katsina

- Rahoto ya bayyana cewa, akalla mutane 11 'yan bindiga suka hallaka a wani yankin jihar Katsina

- Hakazalika sun jikkata akalla mutane uku yayin harin, a zargin sun zo daukar fansa kan kisan mutanensu

- Sai dai, rundundar 'yan sandan jihar ta ce mutane uku ne aka kashe ba 11 da mazauna suka ambata ba

Akalla mutane 11 ne 'yan bindiga suka kashe yayin da wasu uku suka jikkata a garin Tsatsakiya a karamar hukumar Safana da ke jihar Katsina a ranar Asabar.

An ce mutane ukun da suka jikkata na karbar kulawa a babban asibitin Dutsin-Ma.

Daily Trust ta tattaro cewa maharan sun mamaye garin da misalin karfe 9:30 na safe kuma ana zaton sun zo daukar fansa ne kan kisan da suka yi wa dan leken asirinsu da mazauna yankin suka yi.

KU KARANTA: An Sako Shugaban Miyetti Allah da Aka Sace, Ya Ce Ba 'Yan Bindiga Ne Suka Sace Shi Ba

'Yan bindiga sun kashe mutane 11, sun jikkata 3 a Kauyen Katsina
'Yan bindiga sun kashe mutane 11, sun jikkata 3 a Kauyen Katsina Hoto: emergencydigest.com
Asali: UGC

An kuma tattaro cewa kwanaki hudu kafin harin, wani lamari ya faru a kauyen Hakon Kartakawa inda mazauna kauyen suka gano kuma suka kashe wani mai ba da bayanai ga 'yan bindiga.

Wata majiya ta shaida cewa maharan wadanda suka zo kan babura nan take suka fara harbi ba ji ba gani wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 11.

Irin wadannan hare-haren, an gano cewa hanya ce ta 'yan bindiga don aika sako mai karfi ga mazauna kan ganowa da kashe musu mutanensu.

A halin yanzu, mazauna kauyuka na ci gaba da tserewa, suna barin gidajensu zuwa Dutsin-Ma don neman mafaka saboda tsoron lafiyar su.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar ta Katsina, SP Gambo Isa, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a Katsina, ya ce mutane uku ne kawai suka mutu ba 11 ba kamar yadda mazauna garin suka ruwaito.

KU KARANTA: Jirgin ruwa ya kife, ya hallaka mutane 15, wasu sun nutse a jihar Neja

A wani labarin, Gwamnatin Jihar Katsina a karshen mako ta kwashe mabarata sama da 300 daga wani yanki mallakar Kwalejin Horar da Malamai (ATC) da ke Katsina, Daily Trust ta rahoto.

Kwamishinan wasanni da jin dadin al'umma na jihar, Alhaji Sani Danlami, ya bayyana hakan yayin raba kayan tallafi ga mabaratan da abin ya shafa a tsohuwar gidan gwamnatin Katsina.

Yayin da yake jawabi ga mabaratan, Danlami ya ce gwamnatin jihar ba za ta sake amincewa da halayensu ba na mayar da makarantar gidajensu kamar ‘yan gudun hijira (IDPs).

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel