Mahara Sun Shiga Gida Gida, Sun Yi Wa Mutane Sama da 20 Yankar Rago Suna cikin Barci
- Rahotanni sun ce an kashe mutane sama da 20 a ƙauyen Binper da ke gundumar Bwai a ƙaramar hukumar Mangu ta Jihar Plateau
- Harin ya faru ne ƙasa da mako guda bayan kashe mutane uku da kuma zargin ƙona gidaje tsakanin al’ummar Fulani da Mwaghavul
- Wani ganau ya ce maharan ɗauke da makamai sun shiga gidaje suna kashe mutane yayin da suke barci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Plateau, Nigeria - Wasu miyagun da ake zargin yan bindiga ne sun kashe mutane sama da 20 a ƙauyen Binper da ke gundumar Bwai a ƙaramar hukumar Mangu ta Jihar Plateau.
Harin ya faru ne ƙasa da mako guda bayan kashe mutane uku, yayin da al’ummomin Fulani da Mwaghavul suka zargi juna da ƙona gidaje.

Source: Original
Daily Trust ta rahoto cewa shugaban ƙungiyar Raya Al’ummar Mwaghavul (MDA), Bulus Dabit, ya ce maharan sun mamaye ƙauyen ne da tsakar dare, a lokacin da mutane ke barci.

Kara karanta wannan
Mutane sun mutu da gine gine 2 suka rufta kan ɗaliban Islamiyya da ma'aikata a Kano
An shiga gida-gida an yanka mutane
Wani ganau, Daniel Musa, ya shaida cewa maharan da ke ɗauke da manyan makamai sun rika shiga gida-gida, suna tilasta buɗe ƙofofi tare da farmakarsu suna cikin barci.
Ya ce:
“An kai wa ƙauyenmu hari a daren jiya da kuma safiyar yau Talata. Mutane ɗauke da manyan makamai sun rika shiga gida-gida, suna buɗe ƙofofin mutanen da ke barci tare da yanka su.
“Ya zuwa safiyar yau, mun tabbatar da mutuwar mutane sama da 20, yayin da wasu da dama suka samu munanan raunuka, sannan har yanzu ba a san inda wasu mutanen suke ba,” in ji shi.
Mutane sun aika sako ga yan sanda
Wani mazaunin yankin, John Dalyop, wanda ya tabbatar da faruwar harin, ya bayyana lamarin a matsayin mai matuƙar muni, tare da kira ga kwamishinan yan sanda ya dauki mataki.
“Muna fata da tsammanin sabon Kwamishinan ’Yan Sandan jihar zai ɗauki mataki cikin gaggawa tare da farauto waɗanda suka aikata wannan aika-aika,” in ji shi.

Kara karanta wannan
Abin tausayi: Hatsarin jirgi ya rutsa da manoma a hanyar zuwa gonakinsu a Najeriya
Dalyop ya yi Allah-wadai da harin, yana mai bayyana shi a matsayin na dabbanci, tare da kira ga gwamnatin jihar da ta tarayya da su gaggauta ƙarfafa tsaro a yankunan da ke cikin haɗari a Mangu da sauran sassan Jihar Plateau.

Source: Facebook
Ya ce an kai waɗanda suka samu raunuka zuwa asibitocin da ke kusa domin ba su magani, yayin da shugabannin al’umma da mutanen yankin ke ƙoƙarin gano mutanen da har yanzu ba a san inda suke ba.
Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, jami’an tsaro ba su ce komai kan lamarin ba, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.
Yan bindiga sun kashe yan gida daya
A wani labarin, kun ji cewa wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kashe jami'an sintiri uku, wadanda duk 'yan gida daya ne a jihar Plateau.
Mamatan su ne Dachung Danjuma, Victor Danjuma da Nyam Danjuma, kuma an ce an kashe su nan take bayan maharan sun yi musu kwanton bauna.
Wani mazaunin yankin mai suna Lyop Bitrus ya shaida wa manema labarai cewa 'yan uwan suna sintirin dare ne kamar yadda suka saba domin kare al'umma.
Asali: Legit.ng