Wata Sabuwa: Trump Ya Fitar da Hoton Taswirar Hormuz, Ya Ce Ta Amurka ce
- Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ayyana mashigar ruwan Hormuz a matsayin yankin Amurka a wani sabon saƙo da ya wallafa
- Trump ya wallafa wata taswira mai nuna yankin mashigar Hormuz da wata babbar alama mai launin shuɗi, tare da rubuta cewa 'yankin Amurka'
- Iran ta ce ba za ta sake bude mashigar ba har sai Amurka ta cika wasu sharudan da aka amince da su a wata yarjejeniyar wucin gadi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Washington – Shugaban Amurka, Donald Trump ya kara dagula rikicin da Iran bayan ya ayyana mashigar Hormuz a matsayin yankin Amurka.
Trump ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a ranar Talata, 18 ga Agustan 2026, inda ya saka taswirar yankin da aka yi wa mashigar Hormuz wata babbar alama mai launin shuɗi.

Source: Facebook
A cikin taswirar da White House ta wallafa a Facebook, an rubuta 'yankin Amurka', lamarin da ke zuwa ne yayin da ake ci gaba da takaddama tsakanin Washington da Tehran kan makomar mashigar.
Sharudan Iran kan bude Hormuz
Iran ta bayyana cewa mashigar Hormuz za ta ci gaba da kasancewa a rufe har sai Amurka ta cika wasu sharudan da aka cimma a wata yarjejeniyar wucin gadi.
Babban mai shiga tsakani na Iran, Mohammed Bagher Ghalibaf, ya bayyana cewa daga cikin sharudan akwai dage takunkumin teku da na tattalin arziki, tare da sakin kadarorin Iran da aka daskarar.
The Independent ta wallafa cewa matakin na Iran na zuwa ne yayin da mashigar Hormuz ke ci gaba da kasancewa cibiyar rikicin da ya barke tsakanin Iran da Amurka.

Source: Getty Images
Qatar na jiran yarjejeniyar Iran
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Qatar ya ce masu shiga tsakani suna jiran Iran da Oman su cimma yarjejeniyar tsakaninsu kan mashigar Hormuz.
Kasar Qatar ta kuma sake gayyatar tawagar Iran domin tattauna batun matukan jirgin Iran uku da ake zargin an kama bayan harbo jiragen yaƙin Iran, zargin da Qatar ta musanta.
Qatar ta ce yarjejeniyar da za a cimma kan Hormuz za ta taimaka wajen saukaka komawar Iran da Amurka kan teburin tattaunawa.
A wani bangare kuma, Trump ya yi barazanar kai hari kan Oman, wadda take cikin kawayen Amurka, idan har ta kawo cikas ga kokarinsa na tilasta cimma yarjejeniyar zaman lafiya da Iran.
Farin jinin Trump ya ragu
A wani labarin, mun ruwaito cewa farin jinin Trump ya koma mafi karancin matakin da ya taba kaiwa tun bayan komawarsa fadar White House, kamar yadda wani sabon bincike ya nuna.
Kashi 33 cikin 100 na wadanda aka gudanar da binciken a kansu sun ce sun amince da yadda Trump ke gudanar da mulki, yayin da kashi 64 suka ce ba su amince da shi ba.
Wannan adadi ya ragu daga kashi 35 cikin 100 da aka samu a wani binciken baya, kuma ya yi daidai da mafi karancin farin jinin Trump da aka taba samu a wa'adinsa na farko a watan Disamba 2017.
Asali: Legit.ng

