Ban da Alaka da 'Yan Ta'adda, Janar Abdulsalami Ya Yi Martani Kan Alakanta Shi da Ta'addanci

Ban da Alaka da 'Yan Ta'adda, Janar Abdulsalami Ya Yi Martani Kan Alakanta Shi da Ta'addanci

- Tsohon shugaba a Najeriya ya bayyana fushinsa game da alakanta shi da ta'addanci da aka yi a jihar Neja

- Ya bayyana yadda yada jita-jita da karya a kafafen sada zumunta ke jawo kara tabarbarewar tsaro a Najeriya

- Ya kuma yi kira ga 'yan Najeriya da su san irin bayanan da suke yadawa da karantawa a kafafen sada zumunta

Wani tsohon Shugaba a Najeriya, Janar Abdulsalami A. Abubakar (mai ritaya), ya musanta cewa yana da wata alaka da ‘yan bindiga da kuma duk wata kungiyar 'yan ta’adda a jihar Neja, Daily Trust ta ruwaito.

Ya kuma bayyana rahotannin da ke alakanta shi da ayyukansu a matsayin “labaran karya, marasa tushe.”

A cewar wata sanarwa da aka fitar a Minna, Abdulsalami ya yi zargin cewa wasu kafafen yada labarai sun alakanta shi da wani jirgin sama mai saukar ungulu da aka kama yana kai abinci da makamai ga ’yan bindiga a sassan jihar.

KU KARANTA: Wuf: Hotunan Matashi Bakar Fata da Budurwarsa Farar Fata Ya Jawo Cece-Kuce

Ban da Alaka da 'Yan Ta'adda, Abdulsalami Ya Yi Martani Kan Alakanta Shi da Ta'addanci
Ban da Alaka da 'Yan Ta'adda, Abdulsalami Ya Yi Martani Kan Alakanta Shi da Ta'addanci Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Sanarwar na dauke da sa hannun mai taimaka ma janar Abdulsalami kan harkokin yada labarai, Dakta Yakubu Suleiman.

A cikin sanarwar ya nesanta kansa daga irin wannan "mummunan laifin da bai dace da kowane dan kasa mai kishi ba", yana mai jaddada cewa bisa ka'ida, ya kamata ya yi biris da irin wadannan rahotannin na rashin gaskiya amma dole ne ya kafa hujja.

"Irin wadannan labaran na karya suna jawo kara tabarbarewar yanayin tsaro a kasar kuma bai kamata a lamunta da su ba," in ji shi.

Ya nuna nadamar yadda mutane za su iya yaudaruwa da irin wannan labarin tare da bata sunan mutane da halayensu, ya kara da cewa:

"Ina kira ga 'yan Najeriya da su yi watsi da irin wadannan dabi'un na yaudara kuma su yi taka tsantsan da irin bayanan da suke fitarwa da kuma yada su a kafafen sada zumunta".

Ya kuma bukaci ‘yan Najeriya su ci gaba da aiki tukuru tare da yin addu’a don dorewar zaman lafiya a Najeriya, yana mai cewa babu wata al’umma da za ta iya samun daukaka ba tare da zaman lafiya da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a ba.

KU KARANTA: Fadar Shugaban Kasa: Ku Nishadantu da Bidiyon Shugaba Buhari Na Rera Wakar Bob Maley

A wani labarin, Shugaban karamar hukumar Bogoro na jihar Bauchi, Iliya Habila, ya dakatar da hakimin garin Sabon Layi Kwara, Daniel Salka, kan rikicin da ya yi sanadin mutuwar matarsa, Hajara.

Daraktan Gudanarwa na Majalisar karamar hukumar, Marcus Nehemiah, ya bayyana hakan a wata wasika da ya aike wa hakimin da aka dakatar kuma aka gabatar wa manema labarai a ranar Lahadi, jaridar Punch ta ruwaito.

Ya ce dakatarwar ta fara aiki ne nan take har sai sakamakon binciken ‘yan sanda ya fito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.