Wike Ya Ɗebo da Zafi, Ya Bayyana yadda Tinubu Zai Lashe Zabe cikin Sauki a 2027
- Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana yadda zaben Shugaba Bola Tinubu zai kasance a shekarar 2027
- Wike ya ce rarrabuwar kawunan jam’iyyun adawa da yawan sauya sheka sun raunana su, don haka ba za su iya kalubalantar Tinubu yadda ya kamata ba
- Ministan ya kuma umarci hukumomin Abuja su rusa gidajen da aka gina kan hanyoyin ruwa, yana mai cewa gwamnati na da cikakken ikon siyasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya yi magana game da zaben shugaban kasa a shekarar 227.
Wike ya ce Shugaba Bola Tinubu zai samu saukin lashe zaben shugaban kasa na 2027 fiye da na shekarar 2023.

Source: Twitter
Wike ya bayyana hakan ne yayin da yake duba wuraren da ambaliyar ruwa ta shafa a Abuja, inda ya yi magana kan zaben, cewar Punch.
Wike ya magantu kan ƴan adawa a Najeriya
Ya ce rarrabuwar kawunan jam’iyyun adawa za ta sanya musu wahala wajen hada karfi da kalubalantar Tinubu a zaben shugaban kasa mai zuwa.
Wike ya ce:
“Wannan zaben, wato zaben 2027, zai kasance zabe mafi sauki ga Mai Girma Shugaban Kasa. Zaben 2023 ya kasance mai wahala.
“Wannan zaben, inda aka raunana ‘yan adawa, kun san abin da hakan ke nufi? An rage karfinsu; an gama da su.”
Tsohon gwamnan Rivers ya kara da cewa sauye-sauyen siyasa da sauya sheka sun raunana jam’iyyun adawa kafin babban zaben shekarar 2027 mai zuwa.
Wike ya ce adawa mai inganci tana bukatar shekaru tana gina ingantaccen tsarin siyasa, maimakon yawan sauya jam’iyya domin neman damar tsayawa takara.
Ya ce:
“Domin ku zama adawa da za ta cire gwamnati, dole ne ku kasance adawa mai karfi, mai kuzari, wadda ta shafe shekaru tana shiri.
“Ba adawa ce ke neman jam’iyyar da za ta koma ba. Yau suna zuwa Jam’iyya A. Irin wannan adawa ba za ta taba cin zabe ba.”
Wike ya jaddada cewa Tinubu na da damar lashe zaben 2027, yana mai cewa idan takarar ta kasance tsakaninsa da Tinubu, sakamakon zai kasance bayyananne.
Ministan ya yi watsi da sukar da ‘yan adawa da masu sharhi kan siyasa ke yi, yana mai cewa bayyanarsu a kafafen yada labarai ba za ta canza komai ba.
Ya kara da cewa irin wadannan fitowar kafafen yada labarai ba za ta ba ‘yan adawa damar samun nasarar zaben da suka riga suka sha kaye ba.
Wike ya ce ba wanda zai iya rage muhimmancin abubuwan da gwamnatin Tinubu ta cimma cikin shekaru uku da suka gabata, musamman a Abuja.
Wike ya ce:
“Ba na son mayar da martani ga sharhin siyasa. Ba na son mayar da martani ga mutanen da suke tunanin fitowa kafafen yada labarai zai taimaka musu.
“Babu wanda zai iya rage abin da wannan gwamnati ta yi cikin shekaru uku. Babu wanda zai iya rage shi. Ta yi abin kirki.”
Wike ya suka daga ƴan Arewa
An ji cewa Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ce Cardinal John Onaiyekan ba ya nuna taka tsantsan kan siyasa tun daga zaɓen 2023.
Ƙungiyar Matasan Arewa ta Najeriya ta kare Onaiyekan, tana mai cewa ya faɗi gaskiyar halin ƙuncin da 'yan Najeriya ke ciki.
Kungiyar Middle Belt Forum da CBCN sun kuma tsaya kan matsayinsu cewa ya kamata gwamnati ta saurari koken al'umma.
Asali: Legit.ng


