Harbin Maciji Ya Malamin Addini Yana Tsaka da Wa’azi a Plateau, an Rasa Rayuka

Harbin Maciji Ya Malamin Addini Yana Tsaka da Wa’azi a Plateau, an Rasa Rayuka

  • Rabaran Nankur Kundul, limamin COCIN, ya rasu bayan maciji mai dafi ya sare shi wanda ya tayar da hankulan mabiyansa
  • Abokinsa Rinkyer Asaph ya ce a kalla wasu Kiristoci biyu sun riga sun mutu sakamakon cizon macizai a yankin Gamakai
  • Asaph ya yi gargadin cewa yawaitar mace-macen cizon macizai na iya hana manoma shiga gonakinsu, lamarin da zai iya shafar noma da abinci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gamakai, Plateau - An samu rahoton mutuwar wani limamin cocin Christ in Nations, Rabaran Nankur Kundul a Plateau.

Hakan ya biyo bayan zargin cewa maciji ya sare shi a Gamakai da ke karamar hukumar Lantang ta Kudu.

Fasto ya mutu bayan saran maciji a Plateau
Taswirar jihar Plateau da maciji ya sari fasto a coci. Hoto: Legit.
Source: Original

A cewar wani rahoto da Christian Daily International ta wallafa wanda Punch ta gani, an ce abin ya faru lokacin da Kundul ke wa’azi.

Kara karanta wannan

Cutar Apollo ta ɓarke a wasu jihohin Arewacin Najeriya, ta fara yaɗuwa cikin jama'a

Maciji ya sari fasto yana tsaka da wa'azi

Lamarin ya faru ne a lokacin da yake gudanar da hidimarsa a cocin COCIN da ke kauyen Boltim, Gamakai, lokacin da macijin ya sare shi.

Rahoton ya nakalto wani abokin marigayin, Rinkyer Asaph, wanda ya sanar da mutuwar Kundul a ranar 13 ga Agusta, yana cewa macizai masu dafi sun mamaye yankin.

Asaph ya ce wurin da Kundul yake gudanar da wa’azi ya fuskanci mamayar macizai masu dafi, wadanda ake zargin sun riga sun kashe wasu Kiristoci a yankin.

Ya ce:

“Zuciyata ta cika da bakin ciki saboda rasuwar abokina, Pastor Nankur Peter Kundul na COCIN Boltim, Gamakai, Langtang ta Kudu, wanda cizon maciji ya kashe a Sabon Gida Clinic.
“A kalla wasu Kiristoci biyu sun riga sun rasa rayukansu sakamakon cizon macizai a Gamakai.”
Maciji ya sari fasto har lahira a Plateau
Maciji da ake ganin yana da cikin halittu mafi hatsari a duniya. Hoto: Andrew Lichtenstein.
Source: Getty Images

Yadda Gamakai ya yi kaurin suna kan macizai

Asaph ya bayyana Gamakai a matsayin wata muhimmiyar cibiyar noma a Langtang, inda mafi yawan mazauna yankin ke dogaro da noma wajen samun abinci da kudin shiga.

Kara karanta wannan

Dalibai 4 na makarantar haddar Kur'ani sun mutu lokaci guda a jihar Kano, an gano dalili

Ya yi gargadin cewa karuwar mace-macen da cizon macizai ke haddasawa na iya zama babbar barazana ga harkokin noma a yankin.

A cewarsa, manoma na iya fara kaurace wa gonakinsu saboda fargabar fuskantar macizai masu dafi yayin gudanar da ayyukansu na noma.

Ya ce:

“Mace-macen baya-bayan nan da cizon macizai ya haddasa a Gamakai sun kai wani mataki mai matukar tayar da hankali kuma suna bukatar daukar matakin gaggawa.
“Bai kamata cizon maciji ya zama hukuncin kisa kawai saboda mutum yana rayuwa ko noma a Gamakai ba.”

Lokacin da aka tuntubi rundunar ‘yan sandan Plateau ranar Talata, kakakin rundunar, Alfred Alabo, ya tabbatar cewa jami’an rundunar sun isa wurin da lamarin ya faru.

Sai dai Alabo ya ce za a fitar da cikakkun bayanai ne ta shafukan sada zumunta na rundunar ‘yan sandan Plateau.

Maciji ya sari dan limami a daji

Mun ba ku labarin cewa maciji ya sari Aliyu Abubakar Usman, dan babban limamin Yangoji a daji yayin da ya tsere daga sansanin masu garkuwa da mutane.

Kara karanta wannan

Gobar daji ta mayar da sama ja wur, ana ceto mutanen da suka makale

Wani daga cikin 'yan uwan limamin ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce a halin yanzu Usman yana karbar maganin gargajiya.

A wancan lokacin, limamin da dansa guda daya suna hannun masu garkuwan da suke neman a biya Naira miliyan 10 na fansa kafin su sako su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.