Najeriya Na Bukatar Karin Tauraron Dan Adam don Yakar 'Yan Bindiga, Inji DG NASRDA

Najeriya Na Bukatar Karin Tauraron Dan Adam don Yakar 'Yan Bindiga, Inji DG NASRDA

- Darakta janar a hukumar kula sararin samaniya ta kasa ya koka kan rashin isassun kayan aiki

- Ya bayyana cewa, Najeriya na bukatar karin tauraron dan Adam don yaki da ta'addanci a kasar

- Ya kuma ce bincike ya nuna 'yan bindiga ba sa amfani da wayoyin GSM wajen aikata laifukansu

Hukumar Binciken Sararin Samaniya ta Kasa (NASRDA) a ranar Laraba ta ce rashin isassun tauraron dan adam da sauran kayayyakin aiki na shafar sanya ido kan ‘yan bindiga da sauran masu aikata laifuka da ke barna a kasar.

Sabon Darakta-Janar na Hukumar, Halilu Shaba ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Abuja bayan wata tattaunawa da ma’aikatan hukumar a Abuja, babban birnin kasar, Channels Tv ta ruwaito.

Shaba ya ce 'yan bindiga sun zama masu wayewa a ayyukansu kuma bayanai da hukumar ke samu daga yankuna masu nisa ya nuna cewa 'yan bindigan ba sa amfani da wayoyin GSM.

KU KARANTA: Sojojin Najeriya Sun Yi Nasarar Ceto Mutane 13 a Hannun 'Yan Bindiga a Jihar Kaduna

Najeriya Na Bukatar Karin Tauraron Dan Adam don Yakar 'Yan Bindiga, Inji DG NASRDA
Najeriya Na Bukatar Karin Tauraron Dan Adam don Yakar 'Yan Bindiga, Inji DG NASRDA Hoto: sketchup.com
Asali: UGC

“Tauraron Dan Adam ba tsayayye ba ne a inda ake aikata laifuka. Wannan shine dalilin da yasa tauraron dan adam daya ba zai wadatar ba. Abin da Najeriya ke da shi kenan wasu tauraron dan adam guda biyu da ke yin abubuwa biyu na daban.

“Muna da tauraron dan adam mai daukar hoto mai kyau da kuma tauraron dan adam mai daukar hoto matsakaici.

"Barnar 'yan bindiga kan iya kasancewa a lokacin da tauraron dan adam din ba ya kan iyakokin Najeriya, don haka ne ya sa muke neman karin tauraron dan adam a Najeriya," in ji shi.

Shaba, saboda haka, ya yi kira ga hadin gwiwa tsakanin hukumar da hukumomin tsaro a kasar a bangaren musayar bayanai, musamman lokacin da ake shirin kaddamar da hare-hare a kan masu aikata laifuka.

KU KARANTA: Da Dumi-Dumi: Hukumar Jarrabawar NECO Ta Saki Sakamakon Jarrabawar 2020

A wani labarin, Farfesa Felicia Adebola Adedoyin, marubuciyar taken alkawarin kasa na Najeriya, ta mutu a ranar Asabar bayan gajeriyar rashin lafiya.

Marigayiya Adedoyin wanda aka haifa a ranar 6 ga Nuwamba 1938 itace ta biyu cikin yara shida kuma Gimbiya daga Gidan Iji Ruling na Saki dake karamar hukumar Saki ta Yamma, yankin Oke Ogun na jihar Oyo.

Masaniyar a fannin ilimi, ta samu digirinta na uku a shekarar 1981 daga Jami’ar Legas, Nairaland ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel