Da Gaske Atiku Abubakar Ya Janye wa Peter Obi Takara saboda Zaɓen 2027?
- An yi ta yada wasu rahotanni da suka cika kafofin sadarwa cewa Atiku Abubakar ya janyewa Peter Obi takara
- Mai taimaka wa Atiku kan harkokin yaɗa labarai, Paul Ibe, ya musanta ikirarin, yana mai cewa labarin karya ne
- Bincike ya gano cewa babu wata sanarwa daga Atiku ko jam’iyyar ADC da ke tabbatar da cewa ya janye takararsa domin mara wa Peter Obi baya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja- Wani saƙo da ke yawo a kafofin sadarwa ya yi ikirarin cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya janye takararsa a 2027.
An ce Atiku ya janye ne domin mara wa Peter Obi baya gabanin zaɓen shugaban ƙasa na 2027 da ke tafe.

Source: Facebook
Mai taimaka wa Atiku kan harkokin yaɗa labarai, Paul Ibe, ya musanta shi kai tsaye, yana mai cewa “labarin karya ne".

Kara karanta wannan
Duk da shan wahala a zaɓen Osun, Davido ya faɗi yadda Tinubu zai yi nasara a 2027
Rahoton da ake yadawa kan takarar Atiku, Obi
Rahoto ya ce Atiku ya ɗauki matakin ne domin taimakawa wajen kayar da Shugaba Bola Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
An wallafa irin wannan saƙo a wasu shafuka daban-daban, kuma ya samu sama da hulɗa 1,000 daga masu amfani da kafar.
Lamarin ya zo ne a lokacin da ake ci gaba da tattaunawa da shirye-shiryen siyasa tsakanin manyan ‘yan adawa gabanin zaɓen 2027.
Atiku da Peter Obi na daga cikin fitattun ‘yan siyasar adawa a Najeriya, lamarin da ke sa ikirarin haɗin kansu ya bazu cikin sauri a kafafen sada zumunta.

Source: Twitter
Gaskiyar rahoton da ake yaɗawa
Sai dai Dubawa ta yi bincike amma ba ta samu wata sanarwa daga Atiku da ke tabbatar da wannan mataki ba.
Wannan bayani kai tsaye ya nuna cewa ikirarin da ke cewa Atiku ya yanke shawarar janye daga takarar domin Peter Obi ba gaskiya ba ne.

Kara karanta wannan
Magana ta fito: Yadda addinin Tinubu ya hana shi zama abokin takarar Atiku a zaben 2007
Binciken ya kuma duba hanyoyin sadarwa na hukuma da shafukan sada zumunta na Atiku Abubakar da jam’iyyar ADC, amma ba ta samu irin wannan sanarwa ba.
Babu wata sanarwa da aka wallafa a waɗannan shafuka da ke cewa Atiku ya janye daga takara ko kuma ya amince da Peter Obi.
A watan Oktoban 2025, mai taimaka wa Atiku kan harkokin yaɗa labarai ya kuma musanta rahotannin cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasar zai janye domin wani ɗan takarar shugaban ƙasa.
Paul Ibe ya ce bayan duba wata hira da Atiku, tsohon mataimakin shugaban ƙasar bai faɗi ko ya nuna cewa zai janye domin wani ba.
Binciken ya kuma gano wata tsohuwar hira a Arise News mai taken “Arise Exclusive with Atiku Abubakar”, inda ya nuna cewa zai mara wa duk wanda ya lashe takarar haɗin kan ‘yan adawa baya.
Atiku ya magantu kan daukar Tinubu mataimakinsa
A wani labarin, an ji cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya tuna dalilin da ya sa ya ƙi zaɓar Bola Ahmed Tinubu a matsayin mataimakinsa a 2007.

Kara karanta wannan
Abin tausayi: Hatsarin jirgi ya rutsa da manoma a hanyar zuwa gonakinsu a Najeriya
Atiku, wanda ke neman zama shugaban kasa karkashin inuwar ADC a 2027, ya ce ya ɗauki matakin ne domin kare muradun Najeriya.
Ya kuma bayyana yadda daga baya ya goyi bayan Muhammadu Buhari bisa sharadin cewa ba za a yi tikitin Musulmi da Musulmi ba.
Asali: Legit.ng