An Dakatar da Hakimin Kauyen da Ya Lakadawa Matarsa Duka Har Ta Mutu a Bauchi

An Dakatar da Hakimin Kauyen da Ya Lakadawa Matarsa Duka Har Ta Mutu a Bauchi

- An dakatar da wani hakimin yanki a jihar Bauchi bayan ya lakadawa matarsa duka har ta mutu

- An ruwaito cewa, tuni shugaban karamar Bogoro ya aika wa hakimin da takardar dakatarwa

- A halin yanzu yana hannun 'yan sanda in da ake ci gaba da bincike kafin a gurfanar dashi

Shugaban karamar hukumar Bogoro na jihar Bauchi, Iliya Habila, ya dakatar da hakimin garin Sabon Layi Kwara, Daniel Salka, kan rikicin da ya yi sanadin mutuwar matarsa, Hajara.

Daraktan Gudanarwa na Majalisar karamar hukumar, Marcus Nehemiah, ya bayyana hakan a wata wasika da ya aike wa hakimin da aka dakatar kuma aka gabatar wa manema labarai a ranar Lahadi, jaridar Punch ta ruwaito.

Ya ce dakatarwar ta fara aiki ne nan take har sai sakamakon binciken ‘yan sanda ya fito.

KU KARANTA: Da dumi-dumi: 'Yan Bindiga Sun Sace Masu Sallar Tahajjud 40 a Jihar Katsina

An Dakatar da Hakimin Kauyen da Ya Lakadawa Matarsa Har Ta Mutu a Bauchi
An Dakatar da Hakimin Kauyen da Ya Lakadawa Matarsa Har Ta Mutu a Bauchi Hoto: bbc.com
Asali: UGC

A cewar Nehemiya, an dakatar da hakimin, wanda ya kasance tsohon Mataimakin Sufeto Janar na 'yan sanda da ya lakada wa matarsa duka har ta mutu a ranar 19 ga Afrilu, 2021.

Ya kara da cewa, rundunar hadin gwiwar 'yan banga da jami'an sashin ayyukan gwamnati ne suka cafke Salka a ranar 26 ga Afrilun 2021 a cikin garin Bayara inda suka mika shi ga 'yan sanda a Bogoro don gudanar da bincike tare da yiwuwar gurfanar da shi.

KU KARANTA: 'Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane 11, Sun Jikkata 3 a Kauyen Katsina

A wani labarin, Iftila'in ya faru ne a karshen mako a jihar Neja, biyo bayan hatsarin jirgin ruwan da ya faru a garin Tijana na karamar hukumar Munya da ke jihar wanda ya kai ga mutuwar mazauna kauye sama da 15 a cikin jirgin ruwan a cikin wani kogi da ke yankin.

Jirgin ruwan ya kife ne da misalin karfe 6:00 na yamma a ranar Asabar lokacin da ake zargin mazauna kauyen sun dawo daga wata kasuwar yankin da ke Zumba a karamar hukumar Shiroro ta jihar.

A cewar Sarkin Kasuwar na Zumba, Malam Adamu Ahmed wanda ya tabbatar da afkuwar lamarin ga Tribune Online, ya ce jirgin na dauke da akalla fasinjoji 60, ciki har da mata da yara lokacin da ya kife saboda wata guguwar iska mai karfin gaske.

Asali: Legit.ng

Online view pixel