Musulunci Ya Samu Karuwa, Tsohon Fitaccen Dan Wasan Real Madrid Ya Musulunta
- An fara yada rahotanni da ke nuna cewa tsohon fitaccen dan wasan kwallon kafa, Roberto Carlos, ya rungumi addinin Musulunci a Brazil
- Wani ɗan majalisar Turkiyya ya ce jagoran musulmi a Brazil, Sheikh Jihad Hammadeh ya gabbatar masa da musuluntar Carlos
- Har yanzu Roberto Carlos bai tabbatar da musuluntar tasa a bainar jama’a ba, amma dai rahotannin sun fara karfi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Brazil - Rahotanni daga Brazil da kasar Turkiyya sun nuna cewa fitaccen tsohon ɗan wasan ƙwallon ƙafa, Roberto Carlos ya karbi addinin musulunci.
Carlos, wanda ya taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid da kungiyar Fenerbahçe, Roberto Carlos, ya rungumi Musulunci ne a Brazil kimanin makonni huɗu da suka gabata.

Source: Getty Images
Tashar TRT Hausa ta ruwaito cewa wani ɗan majalisar dokokin Turkiyya, Ali Şahin, na jam’iyyar AK mai mulkin ƙasar, ne ya bayyana hakan bayan ganawa da wakilan al’ummar Musulmin Brazil a São Paulo.

Kara karanta wannan
Dalibai 4 na makarantar haddar Kur'ani sun mutu lokaci guda a jihar Kano, an gano dalili
Yadda labarin musuluntar Carlos ya fito
Şahin ya ce ya samu labarin musuluntar Carlos ne daga bakin Sheikh Jihad Hammadeh, wani fitaccen jagora a cikin al’ummar Musulmi na kasar Brazil.
Bayanai sun nuna cewa Hammadeh, shi ne mataimakin shugaban Kwamitin Fatawar Addinin Musulunci ta Ƙasa (ANAJI) kuma mai ba da shawara kan harkokin addini.
A cewar Şahin, Hammadeh ya bayyana masa cewa Carlos ya daɗe yana hulɗa da shi, kuma ya ziyarce shi kimanin makonni huɗu da suka gabata.
Ya ce a lokacin ziyarar ne tsohon ɗan wasan na Real Madrid ya furta kalmar shahada sannan ya rungumi Musulunci.
Dan Majalisar Turkiyya ya taya Carlos murna bisa yadda aka ruwaito ya rungumi Musulunci, tare da yi masa fatan zaman lafiya, lafiya da wadata.
Tauraruwar Carlos ta haska a Real Madrid
Carlos dai ya yi fice a lokacin da yake buga kwallon kafa musamman a tsawon lokacin da ya shafe yana murza leda a kungiyar Real Madrid ta kasar Sifaniya.
A baya-bayan nan ne Roberto Carlos ya auri Suhayla At Tohiri, wata fitacciyar wakiliyar ƙwallon ƙafa ’yar asalin Maroko da ke zaune a Sifaniya.
Carlos, mai shekaru 53, ana ɗaukarsa ɗaya daga cikin manyan ’yan baya na hagu a tarihin ƙwallon ƙafa.

Source: Getty Images
Dan wasan Brazil ɗin ya shafe mafi yawan rayuwarsa ta ƙwallon ƙafa a Real Madrid kafin ya koma Fenerbahçe ta Turkiyya a shekarar 2007.
Sai dai har yanzu Roberto Carlos da kansa bai tabbatar a bainar jama’a cewa ya rungumi Musulunci ba.
Ronaldo ya furta Bismillah
A wani labarin, kun ji cewa wani bidiyo ya bazu a kafafen sada zumunta bayan an ga Cristiano Ronaldo yana furta kalmar "Bismillah" kafin ya zura kwallo a bugun fenariti.
Masu sharhi a kafafen sada zumunta sun yi ikirarin cewa Ronaldo.ya maimaita kalmar sau biyu kafin ya buga ƙwallon da ya zura a ragar Croatia.
Wasu rahotanni sun yi ikirarin cewa Ronaldo ya maimaita kalmar, wadda Musulmi ke furtawa kafin fara wani muhimmin aiki, sau biyunkafin ya buga ƙwallon.
Asali: Legit.ng
