Yadda Matasa Ke Shan Muggan Kwaoyoyi Don Ragewa Yunwa Karfi a Ramadana
- Bincike ya bayyana yadda wasu matasa ke kwankwadar muggan kwayoyi don rage wahalar azumi a Ramadan
- Wasu da dama sun shaida cewa, sukan sha muggan kwayoyi domin su yi bacci da rana don rage radadin yunwa a lokacin azumi
- Malamai, likita da hukumar Hisbah sun yi kira kan lamarin, tare da shawo kan matasa da su daina dabi'ar shan kwaya
Wasu matasa musulmai suna shaye-shayen muggan kwayoyi domin danne tasirin wahalar azumi a watan Ramadan.
Wasu daga cikin matasa suna ci gaba da shan kwayoyi masu karfi kamar codeine da tramadol a lokacin Sahurr don su iya kaucewa azabar yunwa da rana.
Daya daga cikinsu, wata budurwa da ta nemi a sakaya sunanta, ta fada wa Daily Trust cewa ko a cikin Ramadan ta kan sha codeine da kwaya.
"A gaskiya, ina shan Codeine a lokacin Sahur di na. Idan ban sha ba, zan sha wahala sosai," in ji ta, in da ta kara da cewa za ta iya jure yunwar azumin ne kadai idan ta na bacci tsawon wunin, kuma wannan shi ne abin da codeine ke bayarwa ta.
Wani mutumin da ya bayyana cewa ya dade yana shan kwaya ya ce tun lokacin da aka fara azumin Ramadana bai sha wani magani ba, amma ya san da yawa daga cikin ’yan uwansa masu shaye-shayen da har yanzu suke shan kwayoyi yayin azumi.
“Na jarabtu da shaye-shaye; duk da haka, a wannan watan na Ramadan na daina shan komai don ba ni damar mai da hankali sosai kan Ibada,” inji shi.
KU KARANTA: An Sako Shugaban Miyetti Allah da Aka Sace, Ya Ce Ba 'Yan Bindiga Ne Suka Sace Shi Ba
Ya ce wasu daga cikin masu ta'ammali da kwayoyi na yin sahur da kwaya ne don danne yunwa.
“Idan ka sha kwalba daya ta Codeine zaka yi bacci tsawon wuni. Kuma da zarar ka yi bacci, ba za ku yi tunanin shan kwayoyi ko wani abu ba,” inji shi.
Ya kuma bayyana cewa wasu matasa suna buda baki da kwayoyi.
“Na san wasu mutane da ke shan kwayoyi yayin buda baki. Suna buda baki da tabar wiwi ko codeine,” inji shi.
Wani mutumin da bai so a bayyana sunansa ba ya ce matasa sukan sha kwayoyi don rage tasirin azumi.
“Suna yawan shan shi bayan sun ci abinci, sai su kwashe awowi suna bacci; idan sun farka, to lokaci yayi nisa. Don haka azumi ya zama sauki a gare su,” in ji shi.
Dr Auwal Salihu, wani kwararre kan ilimin tabin hankali a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano, ya ce yawan shan kwayoyi ba gaira ba dalili yana da matukar hadari.
“Shan kwayoyi na da matukar hadari ga lafiyar mutum. Ko da yake, hadarin ya dogara da nau'in kwayoyin da mutum zai sha.
"Idan mutum ya fara shan kwayoyi lokaci zuwa lokaci, kamar guda daya a rana sannan daga baya, biyu, kafin ya sani, zai zama masa jiki; ma'ana dole ne ya sha a kowace rana," inji shi.
Ya kara da cewa shan wadannan magunguna na shafar kwakwalwa, wanda ke nufin mai shan miyagun kwayoyi zai yi wasu abubuwa ba daidai ba saboda ya fita a hayyacinsa.
"Yana shafar dukkan jiki, ba kawai kwakwalwa kadai ba," in ji shi.
Game da matasa masu shan kwayoyi don gujewa tasirin azumi, likitan ya ce hakan ba shi da kyau ga lafiya saboda mutum ya kan takura kwakwalwarsa ta hanyar kin ba ta damar yin aikinta.
Ya kara da cewa babu wani sinadari da yake da karfin da zai maye gurbin abinci, amma akwai abubuwa da yawa da suke sanya mutum kada ya yi tunanin abinci ko ya ji yunwa.
“Kun ga, wadannan mutanen da ke shan kwayoyi ba sa kara kiban komai sam kamar yadda ba sa cin abinci. Suna fama da yunwa,” ya kara da cewa.
Ya yi kira ga matasa da su guji shan miyagun kwayoyi saboda lafiyar su.
“Kirana ga matasa koyaushe shi ne su san cewa wadannan abubuwa da suke sha yana raunana garkuwar jikinsu da kara hadarin rashin lafiya da kamuwa da cuta.
"Bayan haka, yana zubar musu da mutunci saboda ana ganin su a matsayin mutane marasa kamun kai a cikin al'umma,” inji shi.
KU KARANTA: Kwanaki kadan bayan sace ta, an sako dalibar jami'ar jiha ta Abia da aka sace
A bangaren addini, wasu malaman da suka yi magana kan matsayin masu shan kwayoyi a lokacin azumi a cikin addinin Islama sun yi Allah wadai da dabi'ar, suna masu cewa abin kyama ne (Makruh).
Shugaban majalisar malamai ta jihar Kano, Sheikh Ibrahim Khaleel ya ce, “Ba za mu iya cewa azuminsu bai karbu ba a Musulunci.
"Zamu iya cewa kawai abinda suka aikata ya sabawa koyarwar musulunci saboda a musulunci mutum yakamata yayi azumi a cikin hankalinsa. Wadannan mutane kuwa suna nasu azumin suna bacci don danne yunwarsu ko don gujewa jarabar ci ko sha," in ji shi.
Wani malami, Dr Yahaya Tanko shi ma ya ce, “Ibada ya kamata a yi ta lokacin da mutum ya ke farke. Ba zai yiwu mutum ya yi ibada yayin da yake bacci ba. Don haka azuminsu abin tambaya ne.”
A nasa bangaren, babban kwamandan hukumar Hisbah, Dr Harun Ibn Sina, ya yi kira ga wadanda ke shan kwayoyi a lokacin Ramadan da su ji tsoron Allah su daina aikata hakan, duk da cewa Hukumar ba za ta iya gano su ba.
“Muna kira ga wadannan mutane da su ji tsoron Allah su daina. Ya kamata su tuna cewa ladar duk wani abu na ibada ana ninka shi, haka nan zunubi,” inji shi.
KU KARANTA: Rundunar 'yan sanda ta cafke mutum 8 da ake zargin Masu Garkuwa da Mutane Ne
A wani labarin, Watan Ramadana, watan da Allah ya saukar da Al-Kur'ani mai girma wata ne mai falala daga cikin watannin musulunci. A watan Ramadana ne Allah ya kebe ibadar Azumi, wacce ya ce shi ke ba da lada gareta na musamman.
Hakazalika, a watan Ramadana Allah ya kebe wani dare mai daraja, wato daren Lailatul Qadari. Kur'ani ya siffanta daren da kwatankwacin dare 1000. Daren Lailatul Qadari na zuwa ne cikin goman karshe na watan Ramadana.
Hakan yasa hadisai da dama ke magana kan a yawaita ibada da tsayuwar salloli cikin dare domin dacewa da daren Lailatul Qadari.
Asali: Legit.ng