Da Dumi-Dumi: An Sanar Cewa Ba A Ga Watan Karamar Sallah Ba a Najeriya

Da Dumi-Dumi: An Sanar Cewa Ba A Ga Watan Karamar Sallah Ba a Najeriya

- Sanarwar kwamitin ganin wata a Najeriya ta bayyana cewa, ba a alamar watan Shawwal ba

- An sanar cewa, gobe za a tashi da azumi na 30 domin cike watan Ramadanan bana da zai kai kwanaki 30

- Daga sanarwar, a fahimci cewa, Alhamis, 13 ga watan Mayu za ta kasance ranar karamar sallah

Kwamitin Sarkin Musulmi kan harkokin addini tare da hadin gwiwar Kwamitin Duban Wata a Najeriya sun sanar da cewa ba su samu labarin ganin watan Shawwal a Najeriya ba a yau Talata 11 ga watan Mayun wanda ya yi dai-dai da 29 ga watan Ramadana.

Don haka Sarkin Musulmi, Sultan Muhammad Sa'ad Abubakar CFR, ya ayyana Alhamis 13 ga watan Mayu 2021 a matsayin ranar Sallah kuma 1 ga watan Shawwal.

Sarkin Musulmi ya taya Musulmin Najeriya murna tare da fatan Allah ya yi masu albarka.

KU KARANTA: Yunkurin Fashi a Fadar Shugaban Kasa Ya Nuna Buhari Ba Zai Iya Tsare Najeriya ba, PDP

Da Dumi-Dumi: An Sanar Cewa Ba A Ga Watan Karamar Sallah Ba a Najeriya
Da Dumi-Dumi: An Sanar Cewa Ba A Ga Watan Karamar Sallah Ba a Najeriya Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Sanar da Legit.ng Hausa ta gano a shafin kwamitin na Tuwita ya karanta: "Babu alamar ganin watan Shawwal a Najeriya yau Talata 11 ga Mayu, gobe Laraba 12 ga Mayu shi ne 30 ga Ramadan. Nan gaba kadan za a fitar da wata sanarwa a hukumance daga majalisar.

KU KARANTA: Da Dumi-dumi: Shugaba Buhari Ya Amince da Sabbin Matakan Tsaro a Kudancin Najeriya

A wani labarin, A yau 11 ga watan Mayu ne aka cika kwanaki 29 ana azumtar watan Ramadana mai alfarma, kuma ake sa ran ganin watan Shawwal domin ajiye azumin tare da fara bikin karamar Sallah.

Mun kawo muku jerin kasashen da suka sanar da yin azumi 30, wato sallah karama a wadannan kasashen sai ranar Alhamis 13 ga watan Mayu 2021, kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel