Gwamnatin Katsina Ta Tattara Mabarata Sama da 300 da Suka Tare a Filin Wata Makaranta

Gwamnatin Katsina Ta Tattara Mabarata Sama da 300 da Suka Tare a Filin Wata Makaranta

- Gwamnatin jihar Katsina ta tattara wasu mabarata dake zaune a filin Kwalejin Horar da Malamai

- Gwamnati ta bayyana cewa, ba za ta lamunci zamansu a filin makarantar ba saboda wasu dalilai

- Gwamnatin ta kuma basu tallafin kayan abinci domin su koma gidajensu su kuma bar filin makarantar

Gwamnatin Jihar Katsina a karshen mako ta kwashe mabarata sama da 300 daga wani yanki mallakar Kwalejin Horar da Malamai (ATC) da ke Katsina, Daily Trust ta rahoto.

Kwamishinan wasanni da jin dadin al'umma na jihar, Alhaji Sani Danlami, ya bayyana hakan yayin raba kayan tallafi ga mabaratan da abin ya shafa a tsohuwar gidan gwamnatin Katsina.

Yayin da yake jawabi ga mabaratan, Danlami ya ce gwamnatin jihar ba za ta sake amincewa da halayensu ba na mayar da makarantar gidajensu kamar ‘yan gudun hijira (IDPs).

KU KARANTA: Yadda Matasa Ke Shan Muggan Kwaoyoyi Don Ragewa Yunwa Karfi a Ramadana

Jihar Katsina Ta Tattara Mabarata Sama da 300 Daga a Filin Wata Makaranta
Jihar Katsina Ta Tattara Mabarata Sama da 300 Daga a Filin Wata Makaranta Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Ya ce yawancin mabaratan da suka yi shigar burtu kamar 'yan gudun hijirar, ba su fito daga kananan hukumomin jihar ba, amma gwamnati duk da haka ta yanke shawarar ba wa kowannensu buhun masara a matsayin tallafi domin su koma gidajensu.

"Mun hadu da su a filin ATC da daddare, mun kirga su kuma mun dauki bayanansu, ciki har da sunayensu da kananan hukumomin da suka fito," in ji shi.

Alhaji Danlami ya ce kwashe mutanen ya zama dole kasancewar yanayin yadda mabaratan ke zaune a harabar makarantar ba za a lamunce da shi ba.

“Ba 'yan gudun hijira bane a zahiri kamar yadda akasarin su suka yarda cewa suna zuwa ne kawai don rokon abinci, idan haka ne, mun basu kayan abinci domin su koma gida.

“Gwamnati ba za ta nade hannayenta ta kalle su suna zaune a wannan wurin tare da yaransu ba. Wannan sam sam ba za a lamunce shi ba saboda galibi wasu masu wucewa a kan titi suna hantararsu,” inji shi.

Kwamishinan ya ce 29 daga cikinsu ‘yan asalin Jamhuriyar Nijar ne don haka ya yi kira gare su da su koma kasarsu bayan sun karbi kayayyakin tallafin.

KU KARANTA: Ba Ma Goyon Bayan Biyan Kudin Fansa, In Ji Wata Kungiyar Arewa

A wani labarin, Iftila'in ya faru ne a karshen mako a jihar Neja, biyo bayan hatsarin jirgin ruwan da ya faru a garin Tijana na karamar hukumar Munya da ke jihar wanda ya kai ga mutuwar mazauna kauye sama da 15 a cikin jirgin ruwan a cikin wani kogi da ke yankin.

Jirgin ruwan ya kife ne da misalin karfe 6:00 na yamma a ranar Asabar lokacin da ake zargin mazauna kauyen sun dawo daga wata kasuwar yankin da ke Zumba a karamar hukumar Shiroro ta jihar.

A cewar Sarkin Kasuwar na Zumba, Malam Adamu Ahmed wanda ya tabbatar da afkuwar lamarin ga Tribune Online, ya ce jirgin na dauke da akalla fasinjoji 60, ciki har da mata da yara lokacin da ya kife saboda wata guguwar iska mai karfin gaske.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Tags: