Saboda Ayaba, Wani Soja Ya Bindige Dan Kasuwa a Jihar Zamfara

Saboda Ayaba, Wani Soja Ya Bindige Dan Kasuwa a Jihar Zamfara

- Wani da ake zargin soja ne ya bindige wani mai sayar da 'ya'yan itace har lahira saboda ayaba

- An ruwaito cewa, sojan ya so tafiya da ayabar dan kasuwan, lamarin da ya jawo cece-kuce

- Rundunar 'yan sanda ta bayyana cewa, tana kan bincike kan lamarin don tabbatar da gaskiya

Wani dauke da bindiga da ake zargin soja ne ya harbe wani mai siyar da 'ya'yan itace a Gusau, babban birnin jihar Zamfara, Abdulkadir Musa saboda ya ki barin maharin ya tafi da tarin ayabarsa ba tare da ya biya shi ba.

Mahaifin marigayin, Alhaji Mustafa Musa, ya shaida wa Punch Metro cewa sojoji biyu sun je wurin da dansa ke sayar da ‘ya’yan itace a ranar Lahadi suka sayi ayaba.

A cewarsa, lokacin da sojojin suka biya kudin, sun yi kokarin daukar wani ayaban ba tare da sun biya ba, lamarin da ya haifar da cece-kuce.

KU KARANTA: Ban da Alaka da 'Yan Ta'adda, Janar Abdulsalami Ya Yi Martani Kan Alakanta Shi da Ta'addanci

Fusataccen Soja Ya Bindige Mai Sayar da 'Ya'yan Itace a Kan Ayaba
Fusataccen Soja Ya Bindige Mai Sayar da 'Ya'yan Itace a Kan Ayaba Hoto: esq-law.com
Asali: UGC

Mustafa ya ce, “Sun sayi ayaba mai tarin yawa a kan kudi N300 kuma a maimakon su dauki wanda suka biya, sai suka dauki wani suna son tafiya da shi, amma dana bai ba su damar yin hakan ba.

“Lokacin da suka nace cewa dole sai sun tafi da ayaban, mai sayar da 'ya’yan itacen ya garzaya zuwa ofishin ’yan sanda, wanda yake kusa da inda abin ya faru, kuma ya ba da rahoton lamarin aka kuma kama sojojin biyu, amma an sake su ba da jimawa ba.”

Mustafa ya kara da cewa ba tare da bata lokaci ba aka saki sojojin, daya daga cikinsu ya tafi gida, ya dauko bindiga ya dawo wurin da lamarin ya faru ya harbe mai sayar da ‘ya’yan itacen.

"An harbi dana a baya kuma mun kai shi Asibitin Kwararru na Yariman Bakura, amma abin takaici, ya rasa ransa," in ji Mustafa.

Mahaifin ya kara da cewa ya kai rahoton lamarin ga dukkan hukumomin da abin ya shafa, gami da Hukumar Kare Hakkin Dan Adam, don a dauki mataki a kan sojan da ya kashe dan nasa.

Mustafa ya kara da cewa "Na kai karar lamarin ga hukumomin da abin ya shafa kuma ba zan huta ba har sai an hukunta sojan don ya zama izina ga wasu,"

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda na jihar, SP Mohammed Shehu, ya bayyana cewa rundunar na gudanar da bincike kan lamarin.

"Muna bincike kan batun," in ji Shehu.

KU KARANTA: Jami'ar Greenfield: 'Yan Bindiga Sun Sake Bayyana Sabuwar Bukatarsu Ga Iyayen Dalibai

A wani labarin, Shugaban karamar hukumar Bogoro na jihar Bauchi, Iliya Habila, ya dakatar da hakimin garin Sabon Layi Kwara, Daniel Salka, kan rikicin da ya yi sanadin mutuwar matarsa, Hajara.

Daraktan Gudanarwa na Majalisar karamar hukumar, Marcus Nehemiah, ya bayyana hakan a wata wasika da ya aike wa hakimin da aka dakatar kuma aka gabatar wa manema labarai a ranar Lahadi, jaridar Punch ta ruwaito.

Ya ce dakatarwar ta fara aiki ne nan take har sai sakamakon binciken ‘yan sanda ya fito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel