Sheikh Mahi Ibrahim Inyass Ya Tabbatar da Nadin Sanusi II a Matsayin Khalifan Tijjaniyya

Sheikh Mahi Ibrahim Inyass Ya Tabbatar da Nadin Sanusi II a Matsayin Khalifan Tijjaniyya

- Darikar Tijjaniya ta tabbatar da nadin Sanusi II a matsayin Khalifa na darikar ta Tijjaniya

- A baya cikin watan Maris, an sanar da Sanusi a matsayin Khalifa na darikar Tijjaniya a Najeriya

- An ruwaito cewa, Sheikh Mahi Ibrahim Inyass ne ya tabbatar da nadin nasa a kasar Senegal

Sheikh Mahi Ibrahim Inyass, babban Khalifa na darikar Tijjaniya, ya nada Sanusi Lamido Sanusi II a matsayin Khalifa na darikar Tijjaniya a Najeriya a ranar Lahadi a Senegal.

A watan Maris, an sanar da tsohon sarkin a matsayin Khalifan darikar Tijaniyya a taron shekara-shekara da ake yi a Sakkwato, TheCable ta ruwaito.

Bangarori biyu na darikar sun nada tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) a matsayin Khalifansu a lokacin bikin Mauludin Inyass.

Auwal Shuaib, sakatare-janar na darikar Tijjaniya ta Najeriya, ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa.

KU KARANTA: An Dakatar da Hakimin Kauyen da Ya Lakadawa Matarsa Duka Har Ta Mutu a Bauch

An Tabbatar da Sarki Sanusi a Matsayin Khalifa Tijaniyya, An Mishi Nadi a Senegal
An Tabbatar da Sarki Sanusi a Matsayin Khalifa Tijaniyya, An Mishi Nadi a Senegal Hoto: @voicylens
Asali: Twitter

"Babban Khalifa na Tijjaniyya Sheikh Mahi Ibrahim Inyass, a hukumance yana bayar da sanarwar nada tsohon Sarkin Kano, Alh Muhammad Sanusi II, a matsayin Babban Khalifa a Najeriya," in ji sanarwar.

"Muna rokon Allah Madaukakin Sarki da Ya datar da shi zuwa ga sauke nauyin da ke kansa kuma ya sanya hakan ya zama mai amfani ga dan adam, Amin."

Wannan ci gaban na zuwa ne shekara guda bayan da Abdullahi Ganduje, gwamnan Kano, ya cire Sanusi daga kujerar sarautar Kano.

Kalli hotuna a kasa:

KU KARANTA: Da dumi-dumi: 'Yan Bindiga Sun Sace Masu Sallar Tahajjud 40 a Jihar Katsina

An Tabbatar da Sarki Sanusi a Matsayin Khalifa Tijaniyya, An Mishi Nadi a Senegal
An Tabbatar da Sarki Sanusi a Matsayin Khalifa Tijaniyya, An Mishi Nadi a Senegal Hoto: @voicylens
Asali: Twitter

An Tabbatar da Sarki Sanusi a Matsayin Khalifa Tijaniyya, An Mishi Nadi a Senegal
An Tabbatar da Sarki Sanusi a Matsayin Khalifa Tijaniyya, An Mishi Nadi a Senegal Hoto: @voicylens
Asali: Twitter

A wani labarinTsohon sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II ya yabawa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan cire tallafin man fetur.

Muhammadu Sanusi II ya bayyana cewa matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na karin kudin shan wutar lantarki da man fetur abu ne mai kyau.

Ganin halin tattalin arzikin da aka shiga a sakamakon annobar COVID-19, Malam Sanusi II ya ce ya kamata a gane gwamnati ba sadaka ta fito yi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel