Dama ga Matasa: Hukumar INEC Za Ta Daauki Ma'aikata Miliyan 1.4 a Zaben 2027
- Hukumar zaben Najeriya watau INEC ta ce za ta dauki kusan ma’aikatan wucin gadi miliyan 1.4 a babban zaɓen 2027
- INEC ta bayyana acewa za a tura wadannan ma’aikatan zuwa rumfunan zaɓe sama da 176,000 da ke a faɗin Najeriya
- Hukumar ta ce tana ƙara matakan yaƙi da yaɗa labaran ƙarya da amfani da AI wajen lalata sahihancin zaɓe a kasar nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ce tana shirin daukar kusan ma’aikatan wucin gadi miliyan 1.4 domin gudanar da babban zaɓen 2027.
Hukumar ta bayyana hakan ne ranar Talata da ta wuce lokacin da ta karɓi tawaga daga Cibiyar IRI ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Dan Twining, wadda ta kai ziyara Abuja domin tantance shirye-shiryen INEC.

Source: Facebook
INEC za ta tura ma'aikata rumfunan zabe
Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya ce za a tura ma’aikatan wucin gadin zuwa rumfunan zaɓe sama da 176,000 da ke faɗin ƙasar, kamar yadda The Cable ta ruwaito.
Ya ce hukumar tana kuma ƙarfafa tsarin jigilar kayayyaki, tura kayayyakin zaɓe tun da wuri da inganta haɗin gwiwa da ƙungiyoyin masu jigilar kaya domin tabbatar da cewa an kai kayan zaɓe da ma’aikata cikin lokaci.
Amupitan ya bayyana ziyarar IRI a matsayin wadda ta zo a kan lokaci, musamman bayan kammala zaɓen gwamnan Osun da kuma gabanin fara yaƙin neman zaɓen 2027.
Yadda INEC ta gwada tsarin zabe
Shugaban INEC ya ce zaɓukan gwamna da zaɓukan cike guraben majalisu da aka gudanar a baya-bayan nan sun zama gwaji ga fasaha, kayan aiki da shirye-shiryen tsaro na hukumar.
Ya ce tsarin tantance masu kaɗa ƙuri’a na BVAS da kuma shafin tattara sakamako na IReV sun nuna ingantaccen aiki, inda adadin sakamakon da aka ɗora a zaɓukan baya-bayan nan ya haura kashi 98 cikin 100.
INEC ta yi gargaɗi kan fasahar AI
Amupitan ya bayyana yaɗa bayanan ƙarya, yaɗa bayanan bogi da kuma amfani da fasahar AI ba bisa ƙa’ida ba a matsayin wasu daga cikin sababbin barazanar da ke iya shafar sahihancin zaɓen 2027.

Source: Facebook
Ya ce INEC ta kafa wani sashe na musamman da ya shafi AI domin samar da ƙa’idojin amfani da fasaha yadda ya kamata da kuma yaƙi da bayanan ƙarya da za su iya rage amincewar jama’a da zaɓe.
Shugaban hukumar ya sake jaddada cewa INEC za ta kasance mai tsaka-tsaki kuma ba ta da fifiko ga kowace jam’iyya ko ɗan takara, kamar yadda Guardian ta kawo.
INEC ba ta da dan takara a 2027
A wani rahoton, kun ji cewa INEC ta tabbatar wa ’yan Najeriya da jam’iyyun siyasa cewa ba za ta goyi bayan wani ɗan takara ko wata jam’iyyar siyasa ba a zaɓen 2027.
Shugaban INEC na kasa, Farfesa Joash Amupitan ya ce hukumar za ta kasance alkalin da ba ya sassauci wajen tabbatar da daidaito ga dukkan ’yan takara.
Asali: Legit.ng

