Manyan Makarantun Gombe na Barazanar Yajin Aiki, Sun ba Gwamnati Mako 2
- Kungiyoyin ma’aikatan manyan makarantun gwamnati a Gombe sun bai wa gwamnatin jihar wa’adin kwanaki 14 ta biya musu wasu haƙƙoƙinsu
- Kungiyoyin sun nemi a aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 tare da karin albashin da ya biyo baya da sauran alawus-alawus
- Sun yi gargadin cewa rashin ɗaukar matakan da suka dace cikin wa’adin na iya jawo sabon yajin aiki, har da yajin aikin sai baba-ta-gani
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Gombe – Haɗakar ƙungiyoyin ma’aikatan manyan makarantun jihar Gombe sun bai wa gwamnatin jihar wa’adin kwanaki 14 da ta ɗauki matakan warware matsalolinsu.
Kungiyoyin sun yi gargadin cewa idan gwamnati ba ta ɗauki “matakai na zahiri, waɗanda za a iya tabbatarwa kuma masu ma’ana” wajen warware matsalolin cikin wa’adin ba, za su iya ɗaukar ƙarin mataki.

Source: Facebook
Punch ta wallafa cewa an bayyana wa’adin ne a cikin wata sanarwar haɗin gwiwa da aka samu ranar Talata, bayan taron ƙungiyoyin da aka gudanar ranar Juma’a, 14 ga Agusta.
Abubuwan da kungiyoyin ke nema
Haɗakar ƙungiyoyin, wadda aka fi sani da JOUGTIN, ta ƙunshi kungiyoyin malaman kwalejojin ilimi, malaman kwalejojin kimiyya da fasaha da kuma manyan ma’aikatan manyan makarantun jihar.
Kungiyoyin sun amince da ƙoƙarin Inuwa Yahaya wajen ci gaba da bunƙasa ilimin, amma sun ce har yanzu akwai muhimman batutuwan jin daɗin ma’aikata da ba a warware su ba duk da tattaunawar da aka sha yi da jami’an gwamnati.
Sun ce jinkirin warware matsalolin ya jefa ma’aikata cikin matsin tattalin arziki, ya rage musu kwarin gwiwa wajen aiki, tare da yin illa ga samar da ingantaccen ilimin manyan makarantu.
Daga cikin buƙatunsu akwai aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi na ƙasa na N70,000 da kuma karin albashin da ya biyo bayansa ga ma’aikatan manyan makarantun gwamnati.
Sun kuma nemi a aiwatar da karin albashin kashi 25 da kashi 35 cikin 100 na CONPCASS/CONTISS da aka amince da shi ga ma’aikatan manyan makarantu.

Source: UGC
Sun nemi biyan basussuka
Leadership ta wallafa cewa kungiyoyin sun kuma buƙaci a biya sauran bashin karin albashin da ya biyo bayan mafi ƙarancin albashin N30,000, ciki har da bashin da ya taru.
Sun nemi kuma a biya tallafin albashi da sauran tallafe-tallafen da gwamnati ta amince da su domin rage wa ma’aikata raɗaɗin cire tallafin man fetur da matsin tattalin arziki.
Haka kuma, sun nemi a aiwatar da karin girman ma’aikatan da aka amince da shi tare da biyan bashin kudin karin girman, wanda suka ce wasu daga cikinsu sun shafe shekaru suna taruwa.
Kungiyoyin sun ƙara buƙatar a biya ma’aikatan ƙarin albashin shekara-shekara da suka cancanta, da kuma alawus-alawus na CATA da CONTTA da aka amince da su ga ma’aikatan manyan makarantun gwamnati.
An ba gwamnatin Gombe kwana14
A cikin sanarwar, ƙungiyoyin sun ce rashin biyan waɗannan haƙƙoƙi ya daura wa ma’aikata da iyalansu nauyin kuɗi da ba za a amince da shi ba tsawon shekaru.
Sun ce lamarin ya kuma shafi jin daɗin ma’aikata, kwarin gwiwarsu, ƙwarewar aiki da kuma dangantakar ƙwadago a fannin ilimin manyan makarantu.
Kungiyoyin sun bayyana cewa:
“JOUGTIN ta bai wa gwamnatin jihar Gombe wa’adin kwanaki 14, wanda zai fara daga ranar wannan sanarwa, domin ɗaukar matakai na zahiri, waɗanda za a iya tabbatarwa kuma masu ma’ana wajen warware matsalolin jin daɗin ma’aikata da aka jero a sama.”
ASUU za ta yi yajin aiki
A wani labarin, mun ruwaito cewa reshen ƙungiyar malaman jami’o’i ta ASUU na Jami’ar Jihar Kaduna (KASU) ya ce sama da malamai 200 sun bar jami’ar saboda rashin kyawawan sharudan aiki.
Yayin da ya ke bayani, shugaban ASUU-KASU, Abubakar Abdullahi, ya bayyana cewa yawan malaman da suka bar jami’ar ya haɗa da farfesoshi.
Ya ce malaman sun bai wa gwamnatin jihar Kaduna da hukumomin jami’ar wa’adin mako biyu domin aiwatar da yarjejeniyar, inda suka yi gargadin cewa rashin ɗaukar matakin yajin aiki.
Asali: Legit.ng


