Jerin Kasashen Da Basu Ga Wata Ba, Ba Kuma Za Su Yi Sallar Idi Gobe Laraba Ba

Jerin Kasashen Da Basu Ga Wata Ba, Ba Kuma Za Su Yi Sallar Idi Gobe Laraba Ba

- Ana sa ran ganin watan Shawwal a yau Talata tare da fara shirye-shiryen gudanar da sallah gobe

- Kasashe da dama sun sanar da cewa, za su azumci ranar Laraba don hade kwanaki 30 na watan Ramadana

- Mun kawo kasashen da suka bayyana cewa, zasu tashi da azumi cikon na 30 na watan Ramadana

A yau 11 ga watan Mayu ne aka cika kwanaki 29 ana azumtar watan Ramadana mai alfarma, kuma ake sa ran ganin watan Shawwal domin ajiye azumin tare da fara bikin karamar Sallah.

Mun kawo muku jerin kasashen da suka sanar da yin azumi 30, wato sallah karama a wadannan kasashen sai ranar Alhamis 13 ga watan Mayu 2021, kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

KU KARANTA: 'Yan Kasuwa Sun Tafka Asara Bayan Mummunar Gobara da Ta Yi Kaca-kaca da Kasuwa

Jerin Kasashen Duniya da Ba Za Su Yi Sallar Idi Gobe Laraba Ba
Jerin Kasashen Duniya da Ba Za Su Yi Sallar Idi Gobe Laraba Ba Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Indonesia

Jordan

Malaysia

Qatar

Saudi Arabia

Turkey

Hadaddiyar Daular Larabawa

KU KARANTA: Yunkurin Fashi a Fadar Shugaban Kasa Ya Nuna Buhari Ba Zai Iya Tsare Najeriya ba, PDP

A wani labarin, Wani tsohon Shugaba a Najeriya, Janar Abdulsalami A. Abubakar (mai ritaya), ya musanta cewa yana da wata alaka da ‘yan bindiga da kuma duk wata kungiyar 'yan ta’adda a jihar Neja, Daily Trust ta ruwaito.

Ya kuma bayyana rahotannin da ke alakanta shi da ayyukansu a matsayin “labaran karya, marasa tushe.”

A cewar wata sanarwa da aka fitar a Minna, Abdulsalami ya yi zargin cewa wasu kafafen yada labarai sun alakanta shi da wani jirgin sama mai saukar ungulu da aka kama yana kai abinci da makamai ga ’yan bindiga a sassan jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.