Jami'ar Greenfield: 'Yan Bindiga Sun Sake Bayyana Sabuwar Bukatarsu Ga Iyayen Dalibai
- 'Yan bindigan da suka sace daliban Greenfield sun sake tuntubar iyayen daliban kan batun fansa
- Sun bayyana sabuwar bukatarsu ta biyan kudin fansa bayan wucewar wa'adin da suka bayar a baya
- Rundunar 'yan sanda a jihar ta bayyana cewa, tana kan kokarin ganin daluban sun kubuta lafiya
‘Yan bindigan da suka sace wasu daliban jami’ar Greenfield a jihar Kaduna, sun tuntubi iyayen su don zayyana sabbin bukatunsu.
Da farko sun nemi a basu kudin fansa na naira miliyan 800 wanda iyayen ba za su iya biya ba.
Biyo bayan gazawar iyayen wajen biyan Naira miliyan 800, an kashe biyar daga cikin daliban a cikin makon farko na sace su.
Amma a makon da ya gabata ranar Litinin, wanda ya kitsa harin, Sani Idris Jalingo, wanda aka fi sani da Baleri, ya nemi a ba shi Naira miliyan 100 da babura 10, yana barazanar kashe sauran daliban washegari idan iyayensu ko gwamnati suka kasa biyan bukatunsa.
KU KARANTA: Ban da Alaka da 'Yan Ta'adda, Janar Abdulsalami Ya Yi Martani Kan Alakanta Shi da Ta'addanci
Ko da yake wa'adin da Baleri ya bayar tun daga lokacin ya kare, Daily Trust ta tattaro cewa sun tuntubi iyayen ne daban-daban a ranar Litinin kuma suka bukaci ko wannensu ya biya Naira miliyan 10.
"Sun kira mu a yau (Litinin) kuma sun gaya min cewa idan na biya Naira miliyan 10 a yau, za a sake 'yar'uwata a yau," in ji wani dangin daya daga cikin wadanda abin ya shafa.
An tattaro cewa bayan da 'yan bindigan suka yi barazanar kashe sauran daliban, daya daga cikin iyayen ta tattauna dasu kuma ta biya Naira miliyan 20 don a sako mata danta.
Wata majiya ta shaida cewa mahaifiyar ta bijire wa duk wani yunkuri da jami'an tsaro ke yi don jin ta bakin danta bayan 'yan bindigar sun sake shi.
Amma rundunar ‘yan sanda ta jihar Kaduna ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar, ASP Mohammed Jalige, ta ce 'yan sanda ba su yi kasa a gwiwa ba a kokarin su na ganin an sako sauran daliban.
KU KARANTA: Wuf: Hotunan Matashi Bakar Fata da Budurwarsa Farar Fata Ya Jawo Cece-Kuce
A wani labarin, Shugaban karamar hukumar Bogoro na jihar Bauchi, Iliya Habila, ya dakatar da hakimin garin Sabon Layi Kwara, Daniel Salka, kan rikicin da ya yi sanadin mutuwar matarsa, Hajara.
Daraktan Gudanarwa na Majalisar karamar hukumar, Marcus Nehemiah, ya bayyana hakan a wata wasika da ya aike wa hakimin da aka dakatar kuma aka gabatar wa manema labarai a ranar Lahadi, jaridar Punch ta ruwaito.
Ya ce dakatarwar ta fara aiki ne nan take har sai sakamakon binciken ‘yan sanda ya fito.
Asali: Legit.ng