Ba Ma Goyon Bayan Biyan Kudin Fansa, In Ji Wata Kungiyar Arewa

Ba Ma Goyon Bayan Biyan Kudin Fansa, In Ji Wata Kungiyar Arewa

- Kungiyar tuntuba ta arewa ta bayyana adawar ta ga biyan kudin fansa ga 'yan bindiga da masu satar mutane

- Kungiyar ta kuma godewa wasu 'yan Najeriya da suka bada gudunmawarsu wajen ganin an kubutar daliban Afaka

- Kungiyar ta bayyana matsayinta ne ta bakin sakataren yada labaranta a ranar Asabar da ta gabata

Kungiyar tuntuba ta Arewa (ACF) ta ce tana adawa da biyan kudin fansa ga 'yan bidiga don ganin an sako mutanen da aka sace, TheCable ta ruwaito.

Kungiyar kolin ta zamantakewar al'ummar arewa, ta ce tana goyon bayan tattaunawa da 'yan bindigan.

Emmanuel Yawe, sakataren yada labarai na ACF na kasa, ya bayyana matsayin kungiyar a Kaduna ranar Asabar.

Kamfanin dillancin labarai na NAN ya ruwaito cewa ACF ta gode wa ’yan Najeriya wadanda suka sadaukar da rayukansu a tattaunawar don 'yantar da wadanda ’yan bindgan suka yi garkuwa da su.

KU KARANTA: Jirgin ruwa ya kife, ya hallaka mutane 15, wasu sun nutse a jihar Neja

Ba Ma Goyon Bayan Biyan Kudin Fansa, In Ji Wata Kungiyar Arewa
Ba Ma Goyon Bayan Biyan Kudin Fansa, In Ji Wata Kungiyar Arewa Hoto: zebranewsonline.com
Asali: UGC

Daliban Kwalejin Noma da Ilimin Gandun Daji na Tarayya dake Afaka a jihar Kaduna, sun sake saduwa da danginsu a ranar Juma'a.

An sace daliban ne lokacin da wasu ‘yan bindiga suka far wa makarantarsu a ranar 12 ga Maris.

Ko da yake an yi garkuwa da 39 daga cikinsu yayin harin, amma an saki 10 daga baya yayin da sauran daliban suka sake samun ’yanci a ranar Laraba.

Da take magana game da lamarin, ACF din ta ce: “Mun gode wa Allah da ya ceci rayukansu kuma muna taya danginsu na kusa da na nesa farin ciki.

"Abin takaicinmu shi ne yadda aka yi zargin an biya miliyoyin nairori kafin su sako daliban da aka sace.

Kungiyar ta ACF ta yi kira ga 'yan bindigan da ke rike da wasu mutanen da ba su ji ba ba su gani ba da su sake su ba tare da bata lokaci ba.

"Duk abin da zai iya zama korafin masu satar mutane a kan al'umma, zubar da jinin marasa laifi ba zai zama mafita ba," in ji ACF.

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo shi ma a kwanan baya ya ce biyan kudin fansa ga 'yan bindiga ba shi ne "mafita ba", yana mai cewa hakan yana karfafa satar mutane.

KU KARANTA: Kwanaki kadan bayan sace ta, an sako dalibar jami'ar jiha ta Abia da aka sace

A wani labarin, An sako Shugaban kungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN), reshen jihar Kogi, Wakili Damina da ake zargin an sace a ranar Talata.

Sakataren kungiyar na jihar, Adamu Abubakar, ya shaida wa manema labarai a Lokoja ranar Asabar cewa an saki Damina a Abuja a daren ranar 7 ga Mayu, Premium Times ta rahoto.

Mista Adamu ya ce ta bangaren Mista Damina, wasu mutane da ake zargin sun fito daga daya daga cikin hukumomin tsaro ne suka tafi dashi ba masu satar mutane ba kamar yadda aka yi zargi tun farko.

Asali: Legit.ng

Online view pixel