Obasanjo Ga Buhari: Shawarwari 3 Kwarara Don Magance Matsalar 'Yan Bindiga
- Matsalar tsaro, musamman 'yan bindiga ta zama babbar kalubale ga gwamnatin shugaba Buhari
- Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya shawarci gwamnatin Buhari kan magance matsalar tsaro
- Ya lissafo wasu hanyoyi uku da ya kamata gwamnati ta bi don ganin ta shawo kan matsalolin 'yan bindiga
Yayin da kalubalen rashin tsaro a Najeriya ke ta kara ta'azzara a kowace rana, wanda ke barazana ga hadin kan kasar, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya ba da wasu shawarwari kan yadda za a shawo kan matsalar.
Dattijon ya ba da shawarwarin ne a ranar Laraba, 5 ga watan Mayu lokacin da ya karbi bakuncin mambobin kungiyar kwararru ta kabilar Tibi (TPG) a gidansa da ke Penthouse a cikin Olusegun Obasanjo Presidential Library (OOPL) da ke Abeokuta a jihar Ogun.
Mun kawo bayanan jawabin tsohon shugaban a yayin ziyarar kamar yadda suke kunshe a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa ta fannin yada labarai, Kehinde Akinyemi ya aike wa Legit.ng.
KU KARANTA: Mbaka Bai Bata Ba: Murna Ya Lullube Mabiya Fasto Mbaka Bayan Sake Bayyanarsa
1. Dabarar Karas da Sanda
Don yaki da kalubalen rashin tsaro keke-da-keke, Obasanjo ya ce Najeriya na bukatar amfani da dabarar "karas da sanda".
A saukakakken harshe, dabarar "karas da sanda" na nufin amfani da gwamutsa ba da tukuici da horo don magance matsalar tsaro.
2. Dakatar da biyan fansa
Tsohon shugaban kasa Obasanjo ya ce biyan kudin fansa yana karfafa masu aikata laifi su ci gaba da ayyukansu na ta'addanci.
Yayin da yake sake nanata cewa biyan kudin fansa ba zai iya magance matsalar rashin tsaro ba, tsohon shugaban ya yi zargin cewa gwamnatin Najeriya, da gwamnati mai ci da wacce ta gabata, sun biya kudin fansa amma sun musanta hakan.
3. Yin maganin 'yan bindiga / masu sace mutane
Obasanjo ya ce gwamnati ba za ta ce kawai ba za ta biya fansa ba, ba tare da daukar matakan da suka dace ba.
Ya ce don kaucewa biyan kudin fansa, dole ne gwamnati "ta kasance tana da hanyoyin da za ta magance" kalubalen tsaro.
Dattijon ya kuma nanata cewa dole ne gwamnati ta samar da hanyoyin yin maganin masu satar mutane da 'yan bindiga a madadin biyan kudin fansa.
KU KARANTA: An Kame Tsohuwa Mai Shekaru 80 Da Jikarta Da Laifin Sayar Da Hodar Iblis
A wani labarin, Wasu iyayen daliban da aka sace na Kwalejin Noma da Ilimin Gandun Daji ta Tarayya dake Afaka, jihar Kaduna, sun nemi afuwa ga Ahmad Gumi, fitaccen malamin addinin Islama, kan “zargin karya” da ake yi masa.
A watan Maris, 'yan bindiga sun kai hari kwalejin da ke karamar hukumar Igabi suka yi awon gaba da daliban, amma an kubutar da 172 daga cikinsu, inda 39 ke hannunsu. Daga cikin 39 din da ke hannun 'yan bindiga, 10 sun sake kubuta.
Da take magana a ranar Talata, yayin zanga-zanga a majalisar kasa don sakin ‘ya’yansu, daya daga cikin iyayen ta yi zargin cewa Gumi ya nuna musu wani Bafulatani mai suna Ahmed, wanda ya karbi Naira 800,000 daga wurinsu.
Asali: Legit.ng