An Sako Shugaban Miyetti Allah da Aka Sace, Ya Ce Ba 'Yan Bindiga Ne Suka Sace Shi Ba
- An sako shugaban kungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah a ranar Asabar a babban birnin tarayya, Abuja
- Rahoto ya bayyana cewa, ba 'yan bindiga ne suka sace shi, ana zargin wasu jami'an tsaro ne suka tafi dashi
- Kungiyar ta bayyana godiya ga hukumonin tsaro da sauran jama'a bisa nuna damuwa da goyon baya
An sako Shugaban kungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN), reshen jihar Kogi, Wakili Damina da ake zargin an sace a ranar Talata.
Sakataren kungiyar na jihar, Adamu Abubakar, ya shaida wa manema labarai a Lokoja ranar Asabar cewa an saki Damina a Abuja a daren ranar 7 ga Mayu, Premium Times ta rahoto.
Mista Adamu ya ce ta bangaren Mista Damina, wasu mutane da ake zargin sun fito daga daya daga cikin hukumomin tsaro ne suka tafi dashi ba masu satar mutane ba kamar yadda aka yi zargi tun farko.
Ya ce Mista Damina ya isa gidansa na Chikara da ke jihar Kogi a safiyar ranar Asabar don haduwa da danginsa.
KU KARANTA: Ba abin mamaki bane a wayi gari Boko Haram ta kafa tuta a cikin Aso Rock, Pat Utomi
Idan za a iya tunawa Mista Adamu ya sanar da manema labarai a Lokoja ranar 4 ga watan Mayu, cewa wasu mutane takwas sanye da kayan sojoji sun dauki Mista Damina daga gidansa.
Ya ce da karfin tsiya mutanen suka dauke shi a cikin farar bas suka yi awon gaba dashi.
Ya kuma ce duk kokarin da aka yi na jin ta bakinsa abin ya ci tura domin layukan wayarsa na kashe.
Sai dai sakataren ya ce kungiyar ta kasa ta dauki mataki domin gano dalilin da ya sa aka sako Mista Damina ta irin wannan hanyar.
Ya kuma ce kungiyar ta umarci wani lauya da ya daukaka batun.
Daga nan Mista Adamu ya nuna godiyar kungiyar ga gwamnatin jihar, ‘yan sanda, 'yan jarida da sauran jama’a kan goyon baya da damuwa da suka nuna.
Kwamishinan 'yan sanda na jihar, Ede Ayuba, ya kuma shaida wa manema labarai cewa kokarin gano inda Damina yake kafin a sako shi ya ci tura, ya kuma nuna takaicin yadda aka kasa samunsa ta layin wayarsa.
KU KARANTA: Bayan dakatar da Hadiza Bala Usman, za a fara bincike a ma'aikatar NPA
A wani labarin, Dalibai 27 na Kwalejin Noma da Ilimin Gandun Daji ta Tarayya, Afaka, jihar Kaduna an sake su.
Daya daga cikin mutanen da suka karbi daliban ya tabbatar wa jaridar Daily Trust labarin.
Ya ce kwamitin tattaunawa na Sheikh Abubakar Gumi ne ya taimaka wajen sakin tare da goyon baya daga tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo.
Daliban na daga cikin mutane 37 da aka sace kusan watanni biyu da suka gabata.
Asali: Legit.ng