Jirgin ruwa ya kife, ya hallaka mutane 15, wasu sun nutse a jihar Neja

Jirgin ruwa ya kife, ya hallaka mutane 15, wasu sun nutse a jihar Neja

- Kifewar jwani irgin ruwa ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 15, yayin da wasu suka nutse a wani yankin jihar Neja

- An ruwaito cewa, lamarin ya fuwa ne da yammacin ranar Asabar lokacin da mutanen suka dawo daga kasuwa

- Rahoto ya bayyana cewa, jirgin na dauke da mutane sama 60, ciki har da mata da yara kanana

Iftila'in ya faru ne a karshen mako a jihar Neja, biyo bayan hatsarin jirgin ruwan da ya faru a garin Tijana na karamar hukumar Munya da ke jihar wanda ya kai ga mutuwar mazauna kauye sama da 15 a cikin jirgin ruwan a cikin wani kogi da ke yankin.

Jirgin ruwan ya kife ne da misalin karfe 6:00 na yamma a ranar Asabar lokacin da ake zargin mazauna kauyen sun dawo daga wata kasuwar yankin da ke Zumba a karamar hukumar Shiroro ta jihar.

A cewar Sarkin Kasuwar na Zumba, Malam Adamu Ahmed wanda ya tabbatar da afkuwar lamarin ga Tribune Online, ya ce jirgin na dauke da akalla fasinjoji 60, ciki har da mata da yara lokacin da ya kife saboda wata guguwar iska mai karfin gaske.

KU KARANTA: Rundunar 'yan sanda ta cafke mutum 8 da ake zargin Masu Garkuwa da Mutane Ne

Jirgin ruwa ya kife, ya hallaka mutane 15, wasu sun nutse a jihar Neja
Jirgin ruwa ya kife, ya hallaka mutane 15, wasu sun nutse a jihar Neja Hoto: rea.gov.ng
Asali: UGC

Ya ce daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su akwai wasu wadanda suka dawo gida da a baya suka gudu daga gidajensu tare da yaransu saboda hare-haren ‘yan bindiga

Ya ci gaba da cewa kimanin mutane 17 aka ceto da rai a kokarin wasu amzauna yankin wadanda suka fara kai dauki jim kadan bayan faruwar lamarin biyo bayan kiran neman agaji da wasu da abin ya shafa suka yi a kusa da inda jirgin ya kife.

Sarkin kasuwa ya kuma bayyana yadda matasa suka yi namijin kokari wajen ganin sun ceto mutane daga halaka, tare da kokawa cewa, har yanzu ba a samu wani taimakon gwamnati ba.

KU KARANTA: Sojojin Najeriya Sun Yi Nasarar Ceto Mutane 13 a Hannun 'Yan Bindiga a Jihar Kaduna

A wani labarin, Wata tankar dakon mai dauke da kayan da ake zargin man fetur ne, ta yi hatsari a kan babbar hanyar Mararaba zuwa Abuja da safiyar Talata.

An gano cewa man ya zube daga tankar da ta yi hatsari, yana kwarara ba kakkautawa zuwa shagunan da ke kusa da wuraren mazauna yankin.

Ya ce: “Hatsarin ya faru ne a daren jiya [Litinin] kuma tankar tana dauke da PMS, sai kayan ya zube daga tankar zuwa shaguna da wuraren zama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.