Arewa
Wasu 'yan bindiga da ake zargin 'yan fashi ne sun sace wasu mutane a jihar Kaduna, yayin da kuma suka raunata wani dan acaba da aka ruwaito yana asibiti yanzu.
Kungiyoyin makiyaya ‘yan Arewa sun yi watsi da dokar hana kiwo a fili da gwamnonin kudu suka kafa, suna masu bayyana ta a matsayin wani nau'i na tsoratarwa.
Maimakon shekara daya da ake yi na zaman NYSC, gwamnan jihar Taraba ya bayyana bukatar a mayar da shirin NYSC shekaru biyu domin horar da mambobi kare kansu.
Gamayyar kungiyoyin Arewa sun yi Allah wadai da kudurorin gwamnonin kudu kan cewa dole ne jami'an tsaro su nemi izini daga gwamnan jiha kafin su aiwatar aiki.
'Yan bindiga, sun dira wani sansanin masu fasa duwatsu, sun sace wani mutum tare da hallaka wani. Tuni an binne wanda aka kashe yayin da ake jiran kiransu.
Jihohin kudu goma sha bakwai sun amince baki daya cewa shugaban Najeriya na gaba ya fito daga yankin su, lamarin da zai kawo cikas ga burin manyan yan siyasa.
Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya bayyana aniyar kafa sabuwar jam'iyyar siyasa da za ta ke amsa manufofinsa. Ya zabi gwamnoni uku su jagoranceta.
Wasu iyalai sun bakunci lahira bayan cin tuwon dawa, lamarin, da ya jefa mai gidan cikin damuwa. Mahaifinsu ya ce lamarin ya zo masa kamar wasan kwaikwayo.
Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Yariman Bakura ya bayyana amincewarsa da jagorancin gwamna Matawalle. Ya ce dama gwamna ne ke jagorantar jam'iyyar APC a jiha.
Arewa
Samu kari