Sabon hari: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da wasu yara bayan raba su da mahaifiyarsu a Kaduna

Sabon hari: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da wasu yara bayan raba su da mahaifiyarsu a Kaduna

  • A wani sabon harin 'yan bindiga a jihar Kaduna, an sace wasu mutane shida ciki har da yara kanana
  • Rahoto ya bayyana cewa, an sace mutanen ne a garin Milgoma na karamar hukumar Sabon Gari
  • A yayin harin, an raunata wani dan acaba, wanda a yanzu haka yana karbar kulawar asibiti

Wasu 'yan bindiga sun sace mutane shida ciki har da yara a garin Milgoma da ke karamar hukumar Sabon Gari a jihar Kaduna.

Daily Trust ta tattaro cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 9 na daren Juma’a yayin da 'yan bindigan suka zo da yawa suka afka wa jama'a.

Wani dan acaba da aka kaiwa harin, yanzu haka yana karbar kulawa a asibitin koyarwa na jami’ar Ahmadu Bello dake Shika.

KARANTA WANNAN: Gwamnatin El-Rufa'i Ta Garkame Bankin Fidelity a Kaduna Saboda Kudin Haraji

Sabon hari: 'Yan bindiga sun sake yin awon gaba da wasu yara a jihar Kaduna
'Yan bindiga dauke da makamai | Hoto: dailypost.ng
Asali: Facebook

Wani mazaunin garin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce dan acaban yana kan hanyarsa ta komawa gida ne sai ya ci karo da ‘yan bindigan wadanda suka bude masa wuta.

Kara karanta wannan

Magoya bayan Buhari ba za su taba barin Tinubu ya zama Shugaban Kasa ba – Lamido

Ya ce an saki mahaifiyar yaran da aka sace lokacin da 'yan bindigan suka gano cewa ba za ta iya tafiya da sauri ba.

Ya ce:

“Da farko 'yan bindigan sun sace yaran tare da mahaifiyarsu amma sai suka gano uwar tana da matsala da kafafunta don haka suka bar ta suka tafi tare da yaran. Sauran mutanen uku an sace su ne a cikin yankin.”

Gwamnatin jihar Kaduna da rundunar ‘yan sanda ba su fitar da sanarwa game da lamarin ba. Amma, Jami'in Hulda da Jama'a na rundunar, ASP Mohammed Jalige, ya nemi a ba shi lokaci don tabbatarwa da faruwar lamarin.

Iyayen daliban Bethel sun fusata, sun fatattaki kwamishinan El-Rufai a yankinsu

Samuel Aruwan, Kwamishinan Tsaron Cikin Gida a Jihar Kaduna, ya hadu da fushin iyaye a ranar Litinin lokacin da ya ziyarci Karamar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna.

Kwamishinan ya jagoranci wata tawaga zuwa Maramara a cikin Karamar Hukumar don kan sace daliban Makarantar Sakandaren Betel da aka yi.

Kara karanta wannan

Allah Ya kunyata Abduljabbar tun a duniya - Mallam Muhammad Rijiyar Lemo

Daily Trust ta ruwaito yadda wasu mutane dauke da makamai suka kutsa cikin makarantar da safiyar ranar Litinin inda suka sace dalibai 121 yayin da suka kashe sojoji biyu.

KARANTA WANNAN: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Jami’ai 2 Na Hukumar Shige da Fice Ta ’Immigration’

'Yan Bindiga Sun Kashe Wani Ma'aikacin Fasa Dutse, Sun Yi Awon Gaba da Wani

A wani labarin, Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu satar mutane ne sun kai hari a wani wurin fasa duwatsu a kauyen Ugya da ke karamar hukumar Toto a jihar Nasarawa, inda suka kashe wani ma’aikaci a wurin, Ibrahim Aliyu, tare da yin awon gaba da wani, Abdul Umar Ekuji.

Wani mazaunin yankin, mai suna Salihu ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 4:43 na yamma a ranar Litinin, Daily Trust ta ruwaito.

Wasu ‘yan bindiga dauke da bindigogin AK47 sun mamaye wurin da ake fasa duwatsun, wanda ya ce yana da nisan kilomita biyu da bainar jama’a.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Manyan masu ruwa da tsaki na APC sun marawa Sanata Musa baya domin ya zama Shugabansu na kasa

Asali: Legit.ng

Online view pixel