Gamayyar Arewa Ta Zargi Gwamnonin Kudu da Ba Nnamdi Kanu da Sunday Igboho Mafaka
- Gamayyar kungiyoyin Arewa sun yi kakkausar martani game da maganganun gwamnonin kudu
- Gamayyar ta zargi gwamnonin kudu da goyon bayan aikata ta'addanci a yankunansu na kudanci
- Hakazalika ta bayyana cewa, suna goyon bayan Nnamdi Kanu da Sunday Igboho ta hanyar takaita karfin jami'an tsaro
Gamayyar Kungiyoyin Arewa (CNG) a ranar Talata, 6 ga watan Yuli sun mayar da martani kan batutuwan da Kungiyar Gwamnonin Kudanci suka gabatar yayin taronsu na Litinin, 5 ga watan Yuli a jihar Legas.
Gamayyar ta zargi gwamnonin kudu da:
"Kare masu aikata laifi, masu kone-kone, da masu aikata munanan ayyuka a tsakanin su ta hanyar kalubalantar damar da gwamnatin tarayya ke da ita na tilasta bin doka da oda a dukkan sassan kasar."
KARANTA WANNAN: 'Yan Bindiga Sun Kashe Wani Ma'aikacin Fasa Dutse, Sun Yi Awon Gaba da Wani
Gamayyar ta yi martani da kakkausar murya
CNG tana magana ne musamman game da daya daga cikin kudurorin kungiyar inda ta nemi hukumomin tsaro da su nemu izinin gwamnonin jihohi kafin fara wani aiki a yankinsu.
Kungiyar ta arewa tana kuma magana akan goyon bayan masu neman ballewar a kudu kamar Mazi Nnamdi Kanu wanda a yanzu haka yake hannun gwamnati da kuma Sunday Igboho wanda hukuma ta ayyana farautarsa a baya-bayan nan.
Kakakin CNG, Abdul-Azeez Suleiman, a cikin wata sanarwa da Legit.ng ta gani ya ce:
“Nunuwa da gwamnonin kudu suka yi na ba da garkuwa ga masu aikata laifuka, tunzura kai hare-hare, da lalata rayuka da dukiyoyin wasu 'yan kasa da kadarorin tsaron kasa ya fallasa matakin hadin bakinsu cikin ayyukan kungiyoyin ‘yan ta’adda masu dauke da makamai kudu.
“Goyon bayansu ga cin amanar kasa, ta hanyar amincewa da ayyuka irin wadannan masu tayar da kayar baya karkashin jagorancin irin su Sunday Igboho da Nnamdi Kanu, ta hanyar gargadin jami’an tsaron kasa kan yin aiki a yankin ba tare da samun izini daga gwamnan wata jiha ba, lamari ne da dole ne a ba shi muhimmancin da ya kamata. "
Shugaba Buhari ya jinjina wa jami'an tsaro bisa kame Nnamdi Kanu da farautar Igboho
Fadar shugaban kasa ta jinjinawa hukumomin tsaron Najeriya game da kamun Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar IPOB, da harin da aka kai kwanan nan a gidan Sunday Igboho, dan rajin kare hakkin Yarbawa da ke Ibadan.
A cikin wata sanarwa da ta fito ta hannun mai taimaka wa shugaban kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, fadar shugaban kasar ta kuma yaba wa hukumomin kasashen duniya wadanda suka ba da hadin gwiwarsu ga hukumar bincike ta kasa (NIA) har aka kamo Kanu.
Rahoton ya kara da cewa IPOB, karkashin jagorancin dan yankin kudu maso gabas da ya ke fafutukar ballewa, ta zama kungiyar da ta yi kaurin suna wajen aikata kisan kai da maganganun batanci wadanda za su iya ruruta wutar fitina a Najeriya, jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito.
KARANTA WANNAN: Batun Daukaka Magu: PDP ta zargi shugaba Buhari da goyon bayan cin hanci da rashawa
Ghali Na'Abba Ya Yi Martani Kan Kame Nnamdi Kanu da Farautar Sunday Igboho
A wani labarin, Ghali Na’Abba, tsohon kakakin majalisar wakilai, ya ce yana goyon bayan matakin da gwamnatin tarayya ta dauka a kan Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar IPOB da kuma Sunday Igboho, dan gwagwarmayar kafa kasar Yarbawa, The Cable ta ruwaito.
Na’abba, wanda shine shugaban kungiyar tuntuba ta Najeriya (NCFront), ya fadi hakan ne a matsayin martani ga wata sanarwa daga Olawale Okunniyi, sakataren kungiyar.
Okunniyi ya ce NCFront za ta kare Yarbawa masu zanga-zanga a kotu, biyo bayan kame wasu adadi na masu zanga-zangar a karshen mako a jihar Legas.
Asali: Legit.ng