Awanni Kadan kafin Fara Kamfen, Tinubu da Akpbabio Sun Sa Labule a Abuja
- Shugaban kasa, Bola Tinubu na ganawa da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, a fadar shugaban kasa da ke Abuja
- Sanata Godswill Akpabio ya isa harabar ofishin shugaban kasa da misalin kusan 6:12 na yammacin Talata 18 ga watan Agusta, 2026
- Ganawar na zuwa ne sa’o’i kadan kafin fara yakin neman zaben 2027 a hukumance ranar Laraba, 19 ga Agusta domin fara shirin kada kuri'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, na gudanar da wata ganawar sirri da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, a fadar shugaban kasa da ke Aso Rock, Abuja.
Rahotanni sun bayyana cewa motar Akpabio kirar Mercedes-Benz S-Class ta tsaya a harabar ofishin shugaban kasa da kusan 6:12 na yammacin Talata, 18 ga watan Agusta, 2026.

Source: Twitter
Jaridar Punch ta wallafa cewa a lokacin da Akpabio ya isa fadar, an ce Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a na kasa yana ganawa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Ana ganawa tsakanin Tinubu da Akpabio
The Cable ta ruwaito cewa har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a bayyana batun da shugabannin biyu ke tattaunawa a kai ba, yayin da ake shirin zaman majalisa a ranar Laraba, 19 ga watan Agusta, 2026.
Ganawar ta ranar Talata ta zo ne sa’o’i kadan kafin fara yakin neman zaben babban zaben 2027 a hukumance domin kara zage damtse game da inganta shiri.
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta sanya ranar 19 ga Agusta, 2026 a matsayin ranar fara yakin neman zaben jam’iyyun siyasa gabanin zaben 2027.
Karin jami'ai sun isa Abuja
Daga baya, an hangi dan majalisar Kano, Alasan Ado Doguwa da wasu ministoci biyu sun isa fadar shugaban kasa inda suka shiga tattaunawa da Shugaban Kasa.

Source: Facebook
Duk da ana kallon taron ya zo a lokacin da siyasar Najeriya za ta kara zafi ganin cewa za a fara tallata yan takara a hukumance gobe, ba a ji ko zaman na da alaka da hakan ba.
Har yanzu dai babu wata sanarwa a hukumance da ta bayyana abin da ya sa shugaban kasa da shugaban majalisar dattawa suka gudanar da wannan ganawa ta sirri.
Haka kuma a ranar Laraba ne shugaban kasa zai zauna da ministoci da sauran mukarraban gwamnati a zaman majalisar zartarwa.
Radda ya fadi alherin Tinubu
A baya, kun ji cewa Gwamnan Katsina, Dikko Radda, ya ce sauye-sauyen tattalin arzikin da Shugaba Bola Tinubu ya kawo na taimaka wa jihohi wajen gudanar da T ayyuka.
Radda ya ce gwamnatin Katsina ta aiwatar da ayyuka sama da Naira biliyan 30 ba tare da karɓar lamuni ba, yana mai cewa hakan ya nuna yadda ake cigaba a karkashin mulkin Tinubu.
Gwamnan ya kuma ce samun ’yancin kai na kuɗin ƙananan hukumomi na daga cikin sauye-sauyen da suka taimaka wa jihohi wajen sauke nauyin da ke kansu na kyautatawa al'umma.
Asali: Legit.ng


