Sojojin saman Najeriya sun ragargaji 'yan ta'addan ISWAP, sun kwato makamai

Sojojin saman Najeriya sun ragargaji 'yan ta'addan ISWAP, sun kwato makamai

  • Rundunar sojojin Najeriya sun lalata motocin bindiga mallakar ISWAP a arewa masu gabashin Najeriya
  • Rahoto ya bayyana cewa, an hallaka wasu 'yan ta'addan da dama, yayin da aka rasa wasu sojojin
  • Rundunar sojojin Najeriya ci gaba da samun nasara a kan 'yan ta'adda musamman a arewa maso gabas

Dakarun sojin saman Najeriya sun lalata manyan motocin bindiga guda uku mallakar ‘yan kungiyar ta’addanci ta ISWAP yayin da suke tsallaka hanyar Damaturu zuwa Maiduguri domin aikata barna kan mazauna yankin, Daily Trust ta ruwaito.

Da yake yi wa manema labarai karin bayani a hedikwatar tsaro da ke Abuja ranar Alhamis kan ayyukan sojoji a cikin makonni biyu da suka gabata, Mukaddashin Daraktan, Harkokin Watsa Labarai na Tsaro, Brig Benard Onyeuko, ya ce sojojin sun kashe duk wadanda ke cikin motocin.

Onyeuko ya bayyana cewa, sojojin na sama, wadanda suka gudanar da ayyukan ta amfani da jirage masu saukar ungulu NAF Mi-35, sun yi aiki ne a lokacin da suka samu kiran gaggawa tare da tabbatar da cewa an kwato dukkanin makaman ‘yan ta’addan a yayin samamen.

Kara karanta wannan

Dalla-dalla: Bayanin yadda ake cike fom na neman ayyukan gwamnati 3 da ake dauka yanzu

KARANTA WANNAN: Dalla-dalla: Bayanin yadda ake cike fom na neman ayyukan gwamnati 3 da ake dauka yanzu

Sojoji Sun Lalata Da Motocin Gun 'Yan Ta'addan ISWAP, Sun Kashe' Yan Aiki A Borno
Jirgin yakin sojojin saman Najeriya | Hoto: dailytrust.com
Asali: Facebook

Ya ce:

“A ranar 2 ga watan Yulin 2021 wasu daga cikin 'yan ta’addan BHT/ISWAP suka tsallaka hanyar Damaturu zuwa Maiduguri a cikin manyan motocin bindiga 3 sun kai hari kan fararen hula wadanda ba su ji ba ba su gani ba.
"Bayan samun kiran gaggawa kan lamarin, an tura jirgin sama mai saukar ungulu NA-Mi-35 zuwa wurin kuma an fatattaki 'yan ta'adda.
"An lalata manyan motocin bindigogi 3 tare da galibin wadanda ke ciki, sauran 'yan ta'adda dake guduwa sojojin kasa sun kashe su a yayin samamen kuma sun kwato wasu makamai."

An rasa sojojin Najeriya yayin fatattakar 'yan ta'addan

Babban kwamandan sojan, ya bayyana cewa an rasa wasu daga cikin jami'an sojoji a fafatawar cikin makwannin biyu da suka gabata.

Kakakin na DMO ya kara da cewa:

“Yayin da yanayin tsaro a wasu wurare ya kasance cikin lumana da kwanciyar hankali, wasu wuraren kuma an samu wasu abubuwan da suka faru a tsakanin wannan lokacin.

Kara karanta wannan

Kungiyar IPOB ta kashe sojoji biyu a Enugu — Kakakin Soji

Sojojin Najeriya na ci gaba da samun nasara kan 'yan ta'adda a fadin kasar nan, musamman a yankin arewa masi gabashin Najeriya.

Rahoto daga jaridar Vanguard ya bayyana yadda sojoji suka fatattaki 'yan ta'addan Boko Haram da ISWAP tare da kwato makamai masu yawa.

KARANTA WANNAN: Domin magance matsalar tsaro, Najeriya za ta fara amfani da 'Robot' wajen yakar tsageru

Sojoji sun bazama daji don ceto sarkin Kajuru da iyalansa daga 'yan bindiga

A wani labarin, Sojoji sun mamaye dajin Kaduna don neman Sarkin Kajuru Alhaji Alhassan Adamu da wasu danginsa 10 da aka yi garkuwa da su a karshen mako, The Nation ta ruwaito.

Satar sarki ya biyo bayan sace wasu dalibai da aka yi a wata makaranta duk dai a jihar ta Kaduna, lamarin da ya sake jefa al'umma cikin tsoro.

Jami'an tsaro na aiki don ganin an ceto su. Baya ga sojojin da ke gandun daji, rundunar 'yan sanda ta ce suna sa ran rundunar dabaru ta Babban Sufeto-Janar na 'Yan Sanda zata ba su goyon baya ta fasaha.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan Ta'addan ESN-IPOB Sun Ragargaji Sojoji da Dama a Jihar Enugu

Asali: Legit.ng

Online view pixel