Ana Kokarin Soke NYSC, Amma Gwamna Ya Nemi a Mayar da Shirin NYSC Shekara Biyu

Ana Kokarin Soke NYSC, Amma Gwamna Ya Nemi a Mayar da Shirin NYSC Shekara Biyu

  • Gwamnan jihar Taraba ya shawarci gwamnatin tarayya da ta dauki mataki wajen tabbatar da kare 'yan kasa
  • A shawarin nasa, ya ce ya kamata a mayar da shirin NYSC shekaru biyo domin horar da mambobi yadda za su kare kansu
  • Hakazalika ya nemi a ba mazauna yankunan iyakoki bindigogi da horar dasu yadda za su iya sarrafa bindiga don kare kai

Darius Ishaku, gwamnan jihar Taraba, ya ce shirin bautar kasa na NYSC ya kamata ya zama shiri na shekaru biyu domin mambobin bautar kasa su samu horo irin na soja.

Da yake jawabi yayin wani shiri a gidan Talabijin na Channels a ranar Laraba, gwamnan na Taraba ya ce a karshen horon na sojoji da za a musu, ‘yan bautar kasa za su iya daukar bindigogi don kare kansu.

Ya lura cewa tunda gwamnati ba za ta iya samar da isasshen tsaro ba, ya kamata ‘yan kasa su himmatu don kare kansu.

KARANTA WANNAN: Jami'a a Najeriya ta ce dole dalibai su fara sanya 'Uniform', dalibai sun yi turjiya

Ana Kokarin Soke NYSC, Amma Gwamna Ya Nemi a Mayar da Shirin NYSC Shekara Biyu
Mambobin shirin NYSC | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

A kalamansa, gwamnan cewa ya yi:

"Idan kuka bar ni, NYSC, zan ce ya kamata ya zama shekaru biyu - shekara guda don horon soja na tilas da kuma wata shekara ta zaman ayyukan zamantakewar da suke yi a yanzu."
“[Wannan kenan] domin duk wanda ya kammala karatu a matsayinsa na dan NYSC zai iya sanin yadda ake rike bindiga, zai iya sanin yadda zai kare kansa, kamar yadda ake yi a wasu kasashe kamar a Isra’ila, Lebanon da sauran wurare.
“Dole ne ku sanya jama’arku su kasance masu himma yayin da ba za ku iya samar da tsaro ba. Dole ne ku ba su damar kare kansu. Akwai tsarin mulki ko babu tsarin mulki, dole ne ku rayu."

Ya kamata a horar da mazauna yankunan kan iya yadda za su kare kansu

Gwamnan ya kuma roki gwamnatin tarayya da ta horar da mazauna yankunan kan iyaka kan yadda za su yi amfani da bindiga don su kare kansu daga 'yan bindiga da masu satar mutane.

Ishaku ya ce bai kamata a bar ire-iren wadannan al'ummomi ga iko da kuma mamayar 'yan bindiga ba idan gwamnati ba za ta iya kare su ba, The Cable ta ruwaito.

Ya kara da cewa:

"Hakazalika, zan roki gwamnatin tarayya da cewa wadanda suke a yankunan kan iyaka da kuma kauyukan da ke da wahalar isa, dole ne a koya musu yadda ake amfani da bindiga don kare kansu."
“Bai dace a bar 'yan Adam haka sakaka ba - a cikin ikon wani wanda ke yawo da AK-47. Wannan ba daidai bane. Ya kamata a horar da mutane 10 ko 20 a kowane kauye dake bakin iyakoki.”

KARANTA WANNAN: Iyayen daliban Bethel sun fusata, sun fatattaki kwamishinan El-Rufai a yankinsu

Bayan da kotu ta wanke ta kan batun NYSC, ministar Buhari ta yi martani

A wani labarin, Wata tsohuwar Ministar Kudi Misis Kemi Adeosun ta ce wata Babbar Kotun Tarayya dake Abuja ta tabbatar da gaskiyarta, The Nation ta ruwaito.

Amma duk da haka ta yarda da cewa ta yi matukar bakin ciki game da zarginta da gabatar da takardar NYSC ta bogi.

Ta ce hukuncin da Justis Taiwo Taiwo ya yanke ba nasara ce kawai gare ta kadai ba, nasara ce ga dukkan ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje.

Ta ce za ta kara daukar matakai a lokacin da ya dace don kare mutuncinta.

Bayan zargin gabatar da takardar shaidar bautar kasa ta NYSC ga hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da Majalisar Dokoki ta Kasa don neman tantancewa, tsohuwar Ministar a ranar 14 ga Satumba, 2018 ta yi murabus daga mukaminta.

Amma ta nemi lauyoyi don su fafata a madadinta a Babbar Kotun Tarayya dake Abuja. Kotun a ranar Laraba ta ce bai kamata tsohuwar Ministar ta gabatar da kanta ga shirin hidima ta NYSC ba tun farko.

Asali: Legit.ng

Online view pixel