Da Dumi-Dumi: Jami'an tsaro sun ceto wasu da aka sace ciki har da dalibin makarantar Bethel

Da Dumi-Dumi: Jami'an tsaro sun ceto wasu da aka sace ciki har da dalibin makarantar Bethel

  • Wasu jami'an tsaron 'yan sanda da na sa kai sun ceto wasu mutane uku, ciki har da dalibin Bethel
  • Kakakin rundunar 'yan sanda na jihar Kaduna ne ya tabbatar da ceto dalibin da mutanen uku a yau Talata 13 ga watan Tuli
  • A baya an sace daliban ne a makarantar sakandaren Bethel dake wani yankin Chikun a jihar ta Kaduna

An ceto daya daga cikin daliban makarantar sakandare da aka yi garkuwa da su a karamar hukumar Chikun da ke jihar Kaduna, Channels Tv ta ruwaito.

Jami’an tsaro sun ceto dalibin, Abraham Aniya tare da wasu mutane biyu wadanda ‘yan bindiga suka sace kwanakin baya a hanyar Kaduna zuwa Kachia.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kaduna, Mohammed Jalige ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa a ranar Talata.

KARANTA WANNAN: Tun kafa Najeriya, ba a taba mulki mai kyau kamar na Buhari ba, gwamna Masari ya bayyana dalili

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun gano rashin tasirin hada lamabobin SIM da NIN, ‘yan sanda ba sa iya bin sawun 'yan bindiga

Da Dumi-Dumi: Jami'an tsaro sun ceto wasu da aka sace ciki har da dalibin makarantar Bethel
Jami'an 'yan sandan Najeriya | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Ya ce jami'an 'yan sanda tare da wasu 'yan kungiyar sa kai ta JTF a sintiri na yau da kullum, sun kubutar da mutanen uku da aka sace yayin da suke yawo a cikin dajin cikin gajiya da rauni a kauyen Tsohon Gaya dake karamar hukumar Chikun a ranar Talata.

Jalinge ya bayyana cewa an kwashe wadanda aka ceton kuma an garzaya da su zuwa asibitin ‘yan sanda dake babban birnin jihar, inda a yanzu haka ake ci gaba da aikin farfado da su, daga nan kuma za a mika su ga iyalansu.

A yayin gudanar da bincike, an bayyana sunayen mutane ukun da suka hada da Zaharaddeen Ibrahim, Nura Nuhu da kuma Abraham Aniya.

Kaduna: Sojoji sun bazama daji don ceto sarkin Kajuru da iyalansa daga 'yan bindiga

Sojoji sun mamaye dajin Kaduna don neman Sarkin Kajuru Alhaji Alhassan Adamu da wasu danginsa 10 da aka yi garkuwa da su a karshen mako, The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Hisbah: An kwamushe wasu mutane da ake zargin suna aikata luwadi a jihar Kano

Satar sarki ya biyo bayan sace wasu dalibai da aka yi a wata makaranta duk dai a jihar ta Kaduna, lamarin da ya sake jefa al'umma cikin tsoro.

Jami'an tsaro na aiki don ganin an ceto su. Baya ga sojojin da ke gandun daji, rundunar 'yan sanda ta ce suna sa ran rundunar dabaru ta Babban Sufeto-Janar na 'Yan Sanda zata ba su goyon baya ta fasaha.

KARANTA WANNAN: Malami ya amince Inyamurai su sa ido kan shari'ar Nnamdi Kanu, amma da sharadi

Sabon hari: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da wasu yara bayan raba su da mahaifiyarsu a Kaduna

A wani labarin, Wasu 'yan bindiga sun sace mutane shida ciki har da yara a garin Milgoma da ke karamar hukumar Sabon Gari a jihar Kaduna.

Daily Trust ta tattaro cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 9 na daren Juma’a yayin da 'yan bindigan suka zo da yawa suka afka wa jama'a.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Wata jahar Arewa ta dauki Mafarauta 10,000 domin su zama kari ga hukumomin tsaro

Wani dan acaba da aka kaiwa harin, yanzu haka yana karbar kulawa a asibitin koyarwa na jami’ar Ahmadu Bello dake Shika.

Asali: Legit.ng

Online view pixel