Kwankwaso Ya Yi wa APC Yasa a Kano, Manya a Jam'iyyar Sun Rungumi Kwankwasiyya
- Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya karɓi wasu jiga-jigan APC da suka sauya sheka zuwa NDC a Kano
- Tsohon kansilan mazabar Zango da wasu jiga-jigai a tafiyar APC mai mulki a yankinsu sun yanke kauna da zama a cikin jamiyyar a Kano
- An gano irin tarbar da Kwankwaso ya yi masu yayin da ake harama na fara kamfen da tunkarar babban zaben 2027 a cikin tan watanni masu zuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya kara rage wa APC mutane a jihar Kano.
Sanata Kwankwaso ya karɓi wasu mambobin jam’iyyar APC da suka sauya sheka zuwa NDC a Kano daga mazabar Zango inda suka karbi shahadar Kwankwasiyya.

Source: Facebook
Hadimin dan takarar shugaban kasa, Hon. Saifullahi Hassan ne ya bayyana hakan a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Litinin, 17 ga Agusta, 2026.
Kwankwas ya tarbi yan APC
A cikin sakon, Saifullahi Hassan ya ce daga cikin waɗanda suka sauya sheka akwai Hon. Nasiru Labaran Zage, tsohon kansilan Zango da ke ƙaramar hukumar Birni.
Haka kuma akwai daya daga cikin manyan APC a yankin, Alhaji Saminu Jibrin, tare da wasu mambobin APC daga suka yanke kauna da ci gaba da zama a jam'iyyarsu.
A cewar Saidullahi Hassan, an karɓi sabbin ’yan jam’iyyar a hukumance zuwa cikin NDC, inda aka kuma yi masu ado da jajayen hular Kwankwasiyya, wadda ta zama alamar magoya bayan Kwankwaso.
Jama'a sun yi maraba da sauya sheka
Sauyin shekar ya jawo martani daga wasu masu goyon bayan Kwankwasiyya a kafafen sada zumunta, inda suka bayyana farin cikinsu tare da yi wa sabbin mambobin fatan nasara.

Source: Facebook
Bashir Nasir Labaran ya bayyana farin cikinsa, inda ya rubuta:
“Masha Allah. Na ji dadin hakan sosai. Allah ya kara maka lafiya mahaifina tare da Jagora.”
Shi ma Aminu AbdulRazaq Ali ya ce:
“Kwankwasiyya Amana. Allah yabamu nasara.”
Wani Young Alhaji ya wallafa cewa:
“Ma Sha Allah. Oga dai yana ta kwashe su Jagora."
Sauyin shekar na zuwa ne yayin da jam’iyyun siyasa ke ƙara ƙoƙarin faɗaɗa tasirinsu da samun sabbin mambobi a shirye-shiryen tunkarar zaɓukan da ke tafe.
Yaron Ganduje ya bar Kwankwaso
A baya, kun ji cewa yaron tsohon gwamnan jihar Kano, Abdulaziz Abdullahi Ganduje ya koma jam’iyyar APC wanda dama daga cikin ta ya fito ba da dadewa ba domin hadewa da Kwankwaso.
Shugabannin APC na mazabar Ganduje a karamar hukumar Dawakin Tofa a Kano sun karbe shi ranar Lahadi 16 ga watan Agusta 2026 bayan ya yanke shawarar rabuwa da abokin hamayyar mahaifinsa.
A watan Mayu Abdulaziz ya rungumi NDC duk da mahaifinsa ya rike har shugabancin APC a matakin kasa kuma ana takun saka tsakaninsu bayan rashin fahimta ta siyasa ta gifta a tsakaninsu.
Asali: Legit.ng

